Boko Haram: Fuskokin Ta’addanci
Barnar Da Ta’addanci Ya Haifar
Yadda Aka Hada Wannan Rahoto

FARFADOWA DAGA IBTILA’IN AYYUKAN TA’ADDANCI

Duk da nasarar da dakarun Najeriya ke samu, ta iya yuwuwa sai an kwashe wasu shekaru da dama, kafin a farfado da garuruwan dake yankin Arewa maso Gabashin kasar.

Idan aka ji shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya na magana akan Boko Haram, tamkar ka ce an gama da kungiyar ne baki daya.

A ranar jajiberin Kirsimeti, Buhari ya bayyana cewa dakarun kasar sun karbe ikon makeken dajin  nan na Sambisa, tunga ta karshe ga mayakan, inda ya ce wannan shi ne zango na karshe a yakin  da ake yi da Boko Haram.

Shugaban ya kuma ce babban hafsan rundunar dakarun kasan Najeriya ýan taddan sun arce su na kuma neman maboya.

Kwanaki biyu bayan haka, sai aka samu tagwayen hare-haren bama-bamai da suka auna wata kasuwar shanu dake Maiduguri, birni mafi girma a arewa maos gabashin Najeriya mai yawan jamaár da ta kai miliyn 1.1.

Daya daga cikin maharan ya kasha kansa ne yayin da jamaá suka huce fushinsu akan wata mata daban da kafin ta ta da bam din jikinta.

Babu dai wanda ya dauki alhakin wadannan hare-hare, amma kuma sun yi kama da irin hare-haren da kungiyar ke kaiwa cikin shekaru biyar ta hanyar amfani da mata, wadanda suka yi sanadin mutuwar dubban ýan Najeriya a wuraren taron jamaá.

Kadan dai daga cikin ýan Najeriya suke nuna mamakinsu. Buhari da wanda y agada, wato Goodluck Jonathan sun yi alkawarin kawo karshen kungiyar ta Boko Haram a baya, amma sai Karin hare-haren aka samu a arewa maso gabashin Najeriya.

Idan dai har za a ce wannan yaki da kungiyar ta Boko Haram mai tsatsauran raáyin addinin Islama na samun nasara – duk da cewa ta wata mahangar hakan ne.

To ammam hakan bai kawo karshen wahalhalun da miliyoyin ýan Najeriya suka shiga ba lura da cewa an rusa masu gidajensu sun kuma rasa hanyoyin samun kudadensu ga rashin abinci da ruwan sha da zullumin gudun kada a yi garkuwa da abokansu da ýan uwa.

Sannan ga uwa uba ga fargabar cewa a kowane lokaci wani dan kunar bakin wake zai kai hari a kasuwanninsu ko a tashar mota domin halaka mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Wasu hotunan bidiyo da Muryar Amurka ce kadai ta samu, sun nuna irin rashin imanin wannan kungiyar, inda a wani wuri mai da cike sa mutum cikin kaduwa, aka nuna mayakan na Boko Haram suna zartar da hukuncin bulala akan wasu mutane goma da ake zargin masu safarar kwayoyi ne.

Sannan yayin da alúmar garin ke sowa, an gabatar da wasu mutane goma da ake zargin suke sayar da kwayoyin, wadanda aka yanke masu hukuncin kisa ta hanyar harbin su a zuciya da ka.

Bayan da aka kamala wannan hukunci, daya daga cikin masu zartar da hukunci ya sanar cewa: “Mun zartar da hukuncin Allah yayin da a bayansa jinni ke kwarara a daga jikin wadanda aka kasha.”

Wani shugaban 'yan Boko Haram yana fadawa wasu mazaje, cikinsu har da yaro karami guda daya, wadanda aka zarga da shan kwaya, cewa za a kashe su idan aka sake kama su. (bidiyon Boko Haram)

Bayan da aka kamala wannan hukunci, daya daga cikin masu zartar da hukunci ya sanar cewa: “Mun zartar da hukuncin Allah yayin da a bayansa jinni ke kwarara a daga jikin wadanda aka kasha.

Jacob Zenn, kwararre ne kan harkokin da suka jibinci Afrika a Gidauniyar Jamestown, wacce take birnin Washington DC, ya kuma ce kafin dakarun Najeriya su samu nasara akan mayakan na Boko Haram, sai an kwashe nan da akalla shekaru uku zuwa biyar nan gaba.

A cewarsa, a hakan ma, akwai yuwuwar a fatattaki mayakan zuwa can cikin yankin na arewa maso gabashin Najeriya ta yadda za a rage tasirunsu, ba kamar yadda a da suke barazana ga kasa ba.

Zenn ya kara da cewa, maido da zaman lafiya a arewa maso gabashin Najeriya, inda sama da mutane dubu 18 suka rasa rayukansu daga hare-haren kungiyar Boko Haram tun da rikicin ya barke a shekerara 2009, zai dauki lokaci mai tsawon gaske.

“A duk lokacin da na fadi hakan, ya kan baiwa ýan Najeriya mamaki, amma ina ga za a dauki akalla shekaru 20,”in ji shi. “hakan kuma na nufin an yi asarar wani rukunin wata alúma – akalla a arewa maso gabashin Najeriya.”

Baya ga haka, sake farfado da fannin ilimi shima zai dauki shekaru, domin kungiyar ta Boko Haram wacce ke nufin karatun zamani haramun ne, ta kone makarantu kurmus da dama.

Wani kiyasin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi a kwanan nan kan irin dumbin bukatun da jamaá ke nema a yankin na arewa maso gabashin kasar, ya nuna cewa kananan yara da suka isa shiga makaranta miliyan uku ne ba su da hanyar zuwa makaranta.

“Sai an dauki akalla zangon wata alúma guda kafin a maido da rayuwa yadda take a da saboda irin ukubar da jamaá yankin suka gani.” In ji Zenn.

GARIN DA YA FUSKANCI UKUBAR BOKO HARAM

Manufar Boko Haram, kamar yadda dadadden shugabanta Abubakar Shekau ke fadi a jawabansa na bidiyo, ita ce a kaddamar da jihadi, ta yadda za a kawar da duk wata al’adar yammaci duniya daga Islama da kuma Najeriya, tare da kafa daular Musulunci da za rika gudana karkashin tsatsauran raáyin Islama.

Sai dai a irin koyar da kungiyar ke nunawa, ba ta ragawa Musulmin Najeriya, inda sukan kai hare-hare a Masallatai da garuruwan da mafi rinjayen alúmominsu Musulmi ne.

Idan ka dauki misalin garin Mainok, wanda karamin gari ne mai tafiyar kilomita 60 a yammacin Maudiguri , sau hudu Boko Haram ke kai hari wannan gari tun daga watan Maris shekarar 2014, inda dumbin mutane suka rasa ryukansu a duk lokacin da aka kai hari tare da barnata gidaje da shaguna da makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya da ofishin ýan sanda.

Wani mai fada a ji a garin mai suna Lawan Bukar, ya gayawa Muryar Amurka cewa alúmar garin ba su da yadda za su iya kare kansu.

“A lokacin da Boko Haram take kawo mana hari ta ko’ina, ba mu da wani shiri na tsaro, muna da wani caji ofis ne mai dauke da ýan sanda hudu kacal.” In ji Bukar.

“Sukan zo a duk lokacin da suka bushi iska, sukan kuma kashe mutane su tafi ba tare da wani tanka masu ba. Mun yi fama da irin wadannan hare-hare har na tsawon shekaru biyu zuwa uku, lamarin da ya sa kowa ya fice daga garin…Boko Haram ta kashe akalla mutane 200 a wannan gari.”

Fararen hula sun fara komawa kan babban titin da ya ratsa ta garin Mainok wanda ake sake ginawa a karo na hudu (VOA)

Tun bayan dakarun gwamnatin ta karbo garin a farkon shekarar da ta gabata  ta kuma kafa wani mazaunin sojoji, mutane suka fara komawa, kuma a karo na hudu aka sake gina garin Mainok.

“Shekaru uku ke nan ‘ya’yanmu bas a zuwa makaranta.” In Ji Kyari.

Sai dai abin takaicin shi ne, ba a garin Mainok kadai aka yi irin wannan ta’asa ba, domin da yawa daga wasu yankunan jihar Borno, cibiyar wannan rikici, ba sa zaunuwa.

Gwamna jihar ta Borno, Kashim Shettima ya fadawA Muryar Amurka cewa, wani rahoton babban bankin duniya ya nuna cewa Boko Haram ta ruguza sama gidaje 950,000 a duk fadin jihar, wato kusan kashi 30 na yawan gidajen harin.

Kungiyar ta kuma rusa ajujuwan makarantu 5,000 da kusan asibitoci 200 da kuma wuraren diban ruwa 1,000 tare da gurgunta hanyoyin samar da wutar lantarki.

“Irin barnar da suka yi babu dadin ji.” In Ji Shettima.

Kusan dai za a iya cewa babu wadanda wannan ibtila’i ya fi shafa, kamar mutanen Bama, cibiyar kasuwanci dake kude maso gabashin birnin Maiduguri dake kan iyaka da kasar Kamaru.

Mayakan Boko Haram sun karbe wannan gair mai yawan mutane 300,000 a watan Satumbar shekarar 2014, inda suka maida shi tamkar kufai.

Kusan daruruwa ko kuma watakila ma dubban mutane mayakan kungiyar suka halaka, kafin sauran mutanen garin su arce.

Wani hoton bidiyo mara kyan gani da ya karade shafin yanar gizo, ya nuna yadda ‘yan bindiga suke kwasar mutane a zuwa kan wata gada da ta ratsa ta kan rafin Yedzaram a cikin babbar mota, suke harbinsu a ka kana su hurga su a cikin ruwan.

Ababan more rayuwa a garin na Bam su ma ba su tsira ba, domin an barnata kusan kashi 90, in ji gwamna Shettima.

Wani dan jaridar Muryar Amurka da ya ziyarci yankin  awatan Satumbar bara, ya tabbatar da ikrarin gwamnan, kamar yadda ya gani karara irin illar da Boko Haram ta bari a baya da suka hada kunannun gidaje.

Gwamna Shettima ya kuma yi alkawarin za a sake gina gidajen da aka lalata, ta hanyar amafnin da kaya da ma’aikatan cikin gida, domin rage kaifin matsalar rashin aiki.

“Za mu gina gidaje da makarantu da wuraren shan magani domin kalulabalaci akidar Boko Haram, za kuma mu gina har da masallatai.” In ji shi.

Sai dai duk da haka ababan da ake bukata suna da yawa.

Yara su na diban ruwa a sansanin 'yan gudun hijira da aka kafa cikin garin Bama, sansanin da yake dauke da mutane dubu 27 a lokacin. (VOA)

A Watan Janairu, Hukumar kasa – da kasa dake sa ido kan masu yin kaura, ta fitar da wani rahoto inda ta ruwaito kashi daya cikin ukun muaten miliyan 1.7  da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu suna zaune ne a sansanoni kuma makamncin haka.

Sannan akwai yuwuwar yankunan da ma’aikatan ba da agaji ba za su iya kaiwa gare su ba suna cikin matsalar karancin abinci, a cewar ofishin na Majalisar Dinkin Duniya na OCHA.

Baya ga haka, akwai ‘yan Najeriya miliyan biyar da aka yi kiyasin suna fuskantar “matsanancin matsalar yunwa da rashin abinci mai gina jiki,”, a cewar ofishin.

Sannan a wani yanayi makamancin wannan haka ma lamarin yake a kasar Chadi da Nijar da Kamaru, inda a nan ma kungiyar ta Boko Haram ta kafa sansanoni tare da kai hare-hare tun daga shekarar 2013.

Babu kuma wata alama dake nuna cewa matsalar karancin abinci za ta sauya nan kusa, a wani gargadi da ofishin na Majalisar Dinkin Duniyan na OCHA ya yi yayin da fargabar fashewar nakiyoyin da aka binne ke hana yin ayyukan noma shekara uku a jere.

Shettima ya kuma yaba da yunkurin da hukumar tallafawa kananan yara ta UNICEF da hukumar  samar da abinci ta duniya da hamshakin mai kudin nan Aliko Dangote da taimakon da suka bayar domin ganin mutane sun koma rayuwarsu ta da, sannan a wani yanayi na nuna cewa babu yadda za a bari al’amura su kara dagulewa, Shettima ya yi imanin cewa al’amura za su daidaita.

“A halin da mu ke ciki yanzu ba mu da komai, ba wai ina ruruta lamarin ba ne, koda ma ana zaman lafiya, mutanenmu su ne masu fama da mafi matsanancin talauci a tsakanin talakawa, sannan gas hi Boko Haram ta kara kassarasu.To amma kuma huruminmu ba ne mu yi ta korafi, sai dai mu rika daukan matakan da za su kyautata rayuwarmu.” In ji Shettima a wata hira da ya yi da Muryar Amurka.

To amma kuma ba za a samu damar daukan matakan ci gab aba, muddin gwamnatin Najeriya ba ta hada kai da makwabtanta sun dakile kungiyar ta Boko Haram daga farfadowa ba.

 

“SAU NAWA AKA KASSARA KUNGIYAR TA BOKO HARAM?”

Mafi yawan lokutan da aka kwashe a shekarar 2014, kusan za a iya cewa kungiyar ta Boko Haram ta ci karanta ba babbaka.  A watan Aprilu, kungiyar ta yi garkuwa da ‘yan matan makaranta 2176 a garin Chibok, wadanda mafi aksarinsu ba a san nda suke ba a yau.

Cikin shekarar 2014, kungiyar ta kwace ikon garuruwa a jihohin Borno da Yobe da Adamawa.

A watan Agusta, shugaban kungiyar Shekau ya ayyana kafa daular Musulunci wacce ya tsara gudanar da ita a irin tsauraran fahimtar da suka yi ma Shari’ar Musulunci.

A ranar 15 ga watan Janairun shekarar 2015, daruruwan mayakan kungiyar suka yi kukan kura suka far ma Mauduguri, babban birnin jihar Borno ta kofofi biyu da nufin kwace ikon sa, amma dakarun kasa da na saman Najeriya suka dakile wannan yunkuri.

Mako guda bayan haka, sai mayakan suka sake kawo wani farmaki, amma wannan karo ta kofofi uku, haka dai dakarun Najeriya suka kara kora su tare da taimakon sojojin saman kasar da ‘yan banga – wadanda suka yi amfani da adduna da itatuwa.

Boko Haram: Fararen Hular Da Aka Kashe

Wannan nasara da aka yi akan mayakan na Boko Haram, ta matukar karya lagwansu, kuma cikin ‘yan makwanni dakarun Najeriya tare da taimnakon takwarorinsu na Chadi da Kamaru suka fara fatattakar ‘yan ta’addan zuwa wajen gari.

Sai dai wannan nasara ta yi wa shugaban Najeriya a wancan lokacin shigar sauri, domin a watan Maris ya fadi zabe inda Muhammadu Buhari, wanda tsohon shugaban kasa ne a zamanin mulkin soji, wanda ya gina yakin neman zabensa akan alkawarin kawo karshe kungiyar ta Boko Haram.

Tun bayan da ya karbi mulki, dakarun hadin gwiwa hade da na makwatba sun samu gagarumar nasara, domin har ta kai ga kungiyar ta Boko Haram ba ta rike da wani gari ko birnin a Najeriya baki daya.

Kuma yawan hare-haren kunar bakin wake da sauran hare-hare akan wuraren sojoji sun ragu matuka.

“Kusan zan iya cewa al’amura sun sassauta a yanzu,” domin dakarunmu suna fuskantar harin kwantan bauna ne kawai, in Ji Minsitan tsaron Najeriya Mansru Dan Ali a wata hira da ya yi da Muryar Amurka a farkon watan Janairu.

Sai dai sassautawar al’amura ba ya nufin an samu cikakken zaman lafiya ba ne. Har ya zuwa wannan lokacin mayakan na Boko Haram kan kai hari tare da samun nasara a wasu lokuta.

A watan Nuwamban bara, kungiyar ta kashe wasu manyan sojojin Najeriya a wasu hare-hare kwantan-bauna da ta kai a jihar ta Borno, wadanda suka rutsa har da sojan da ya fi samun lambar yabo, Laftanar Kanar  Muhammadu Abu Ali.

A watan Dismbar bara har ila yau, wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake a garin Madagali sun kashe mutane sama da 50.

Sannan a tsakiyar watan Janairun da ya gabata, wasu ‘yan kunar bakin wake uku, ciki har da matshiya mai shekaru 12, sun kai hari cikin Jami’ar Maiduguri, inda suka halaka wani Farfesa suka kuma raunata mutane 17.

Hade da wadannan hare-hare, a ranar 17 ga watan Janairu sai dakarun saman Najeriya suka jefa jama’ar kasar cikin yanayi na kaduwa bayan da suka jefa bama-bamai akan fararen hula da rikicin na Boko Haram ya tilastawa barin gidajensu a kauyen Rann a jihar ta Borno.

Wani jami’I a yankin y ace fiye da mutane 230 suka mutu a harin na sama, wanda dakarun saman Najeriyar suka ce an kai shi bisa kuskure inda suka yi alkawarin za a binciki ainihin abin da ya faru.

Yanzu haka, dakarun kasa, sun fi maida hankali ne wajen agnin sun kawar da mayakan na Boko Haram daga tungarsu dake cikin dajin Sambisa dake cikin tsaunuka da koguna a wanin yanki dake gefen jihar ta Borno.

Brig. Janar Victor Ezugwu na dakarun Najeriya ya kwatanta yakin da su ke yi da mayakan kungiyar ta Boko Haram a wannan daji tamkar kamar yadda kuliya da bera ke wasa tsere.

'Yan Boko Haram su na yin tambayoyi ma wata mata a bayan da suka kutsa cikin kauyensu dake kusa da garin Banki (bidiyon Boko Haram)

“Abinda ke faruwa shi ne da zaran mun rushe sansanoninsu, sai sauran mayakan su sake haduwa su kafa wasu sansanonin.” In ji Ezguwu.

Ya kara da cewa “A lokacin da muka rusa sansanoninsu watannin biyu da suka gabata, idan mun ka koma mu ka ga alamar an sake zama sai mu sake rushe sansanin. Wadannan sansanoni bas u da wahalar ginawa, bas a kuma bukatar kudade, abinda suke yi shi ne su sami karkashin bishiyoyi ko saman tsaunuka inda akwai rufi, ba sa saka komai a wurin, suna zama ne tamkar dabbobi.”

Baya ga haka, wani bangaren yakin da kungiyar ta Boko Haram, shi ne shugabanta Shekau da ke bayyana a hotnuna bidiyo akai-akai.

Akalla sau uku, dakarun Najeriya suna ikrarin cewa Shekau yam utu – sai kuma a gansa ya bayyana a sabbin bidiyo inda ya kan yi barazana ta hanyar da ya saba – rike da bindigar “Machine Gun” ya na sarar iska tare da yin izgilanci hade da dariya – a wani lokaci da ma yak an yi wani irin kuka kamar tsuntsu.

Kamar yadda halayensa suka nuna a hotunan bidiyo da yake fitarwa, wasu na ganin Shekau zai kyau da dan wasan kwaikwayon barkwanci – idan da a ce bayanai ba sa dauke da munanan kalaman barazanar kisa.

Bidiyo da ya fitar a baya-bayan nan, shi ne wanda aka sake a karshen watan Disambar bara, ya nuna Shekau ya na musanta ikrarin shugaba Buhari  na cewa an fatattaki Boko Haram daga dajin Sambisa.

“Kada ka rika fadawa mutane karya,” Shekau ya ce a harshen Hausa, “idan har kun gama da mu, ta yaya aka ganni a haka, sau nawa kuna kashe mu a irin karyarku?”

'IDAN BA A KAWO KARSHEN NUNA KIYAYYA BA…..'

Gaskiyar maganar ita ce, ba za a iya kawo karshen Boko Haram baki day aba, har sai an magance matsalolin da suka haifar da bullar kungiyar.

Najeriya ita ce kasar da ta fi kowace yawan arzikin mai a nahiyar Afrika da ma arzikin kansa, idan aka laákkalri da irin ababan da take samarwa na cikin gida, sai dai man ya na kudancin kasar ne kuma mutane ne kalilan ne ke cin gajiyarsa.

Mutane da yawa kan alakanta rikicin na Boko Haram da kangin talaucin da ya daibaibaye mutane a arewa maso gabshin Najeriyar, da kuma kin daukan matakin magance hakan da hukumomi ba su yi ba.

Hukumomin Najeriya ba su yi “hobbasan” taimakawa mutanen yankin ba, in ji Zenn, wanda ya dade ya na nazari kan kungiyar Boko Haram.

“Wadannan wurare kauyuka ne dake da nisa, hakan ya sa ba lallai ba ne mutanen yankin su nuna mubaya’arsu ga gwamnati idan aka yi la’akkari da yadda bas a samun ababan more rayuwa.”

Baya ga haka, akwai matsalolin da suka shafi yanayin kasar yankin a cewar Zenn. “Akwai mutane da dama dake rasa hanyoyin shigar kudadensu saboda kwararar hamada, saboda haka, lura da cewa babu ayyukan yi, Boko Haram sai ta zama masu kamar abin yi.

Kamar yadda sauran kungiyoyin masu ta da kayar baya suke a duk fadin Afrika da yankin Gabas ta Tsakiya, kungiyar ta Boko Haram ta fake da inuwar addinin Islama, inda ta yi wa ma’anoninsa mummunar tarjama, ta yadda zai kwadaitar da matasa wadanda ba su da tabbacin samun makoma mai kyau a rayuwarsu.

Wasu hotunan bidiyo da Muryar Amurka ta samu, sun nuna yadda shugabannin wannan kungiya ke gurbata koyarwar adddinin Islama inda suke koyar da wata ma’ana da ta sabawa Isalama.

Daga cikin wadannan hotunan bidiyo akwai wanda aka nuna wani kwamandan kungiyar ta Boko Haram ya na yiwa mayakan kungiyar huduba gabanin wani hari da za su kai.

“Allah ya ce mu yaki wadanda ba su yi imani da addininmu ba.” In ji Kwamndan ya na jaddada cewa, “Idan har ana so a yada addinin Islama, dole sai an zubar da jinni – ko namu ko na wadanda ba su yi imani ba.”

A wani bidiyon kuma, wani dan sako da Shekau ya turo, ya fadawa taron jama’a wannan sako, “Allah ya jarrabe mu da munafukai a cikinmu, duk addinin da ake zaman lafiya da wadanda ba yi imani ba, ba daga annabi ya zo ba.”

Malaman addinin Isalama da suka tattauna da Muryar Amurka sun yi watsi da irin wannan fatawa ta ‘yan Boko Haram.

“Akwai mummunar fahimta tattare da yadda suke fassara koyarwar addinin Islama,” in ji Farfesa Ibrahim Mohammed, Darekta a Cibiyar Nazarin Al Qur’ani na Jami’ar Ado Bayero dake Kano.

Ya kara da cewa, “Akwai rashin daidaito da mummunar fassara kan yadda suke karanta ayoyin Al Qur’ani da kuma yadda suke saka ayoyin ba a inda suka dace ba.”

“Idan ka hada wadannan rassa uku na yadda suke fassara ayoyin, ba za su baka ma’ana ba.”

'Yan gudun hijira daga Kumshe da Banki su na sallah cikin wani masallacin da suka yi a sansanin 'yan gudun hijira na garin Bama (VOA)

Shima shararren Malamin nan na Sufi, Khalifa Abul Fathi dake Maiduguri ya amince cewa mummunar fassara kungiyar ta Boko Haram ke yiwa ayoyin Al Qur’ani.

“Wadanne hanyoyin koyarwar addinin Islama suke bi? Babu kowane! Sun kashe mata sun kashe yara sun kashe wadanda babu ruwansu sun kashe kiristoci a mujami’unsu da gidajensu.” In ji Sheikh Abul Fathi.

A irin hangen da Sheikh Fathi ya yi, ya na ganin kungiyoyi irinsu su Boko Haram za su ci gaba da wanzuwa idan har ba a kawo karshen muhawarar dake tsakanin Musulmi ba – wacce ita take haifar da rarrabuwar kawuna.

“Idan ba mu daina nuna kiyayya a tsakaninmu ba, za a kawo karshen Boko Haram, amma kuma za ka ga wata kungiya ta sake bullowa da wani suna.”

“Da yawa daga cikin mutane na can suna haduwa saboda wata irin akida ta su, dole ne a tunkari wannan akida.” Ya kara da cewa.

Ta iya yuwuwa “wata kungiya” na can tana kokarin fitowa. A shekarar 2015, Shekau ya yi mubaya’a ga kungiyar IS.

Amma kuma a watan Agustan bara, IS ta juya Shekau baya, inda ta nada Abu Musab Al Barnawi – wato dan shugaban da ya kafa kungiyar ta Boko Haram – a matsayin sabon shugaban.

Kwanani biyu bayan haka, Shekau wanda nadin bai masa dadi ba ya fito a wani hoton bidiyo a fusace ya na watsi da nadin al Barnawi lamarin da ya sa cikin wasu ‘yan kwanaki kungiyar ta rarraba – inda har aka yi dauki ba dadi.

Bangarorin  dai suna da akidoji daban-daban, yayin da Al Barnawi ke cewa kungiyar ta mai da hankali wajen kai hare-hare akan kiristoci da dakaru, Shekau cewa ya ke duk wanda ba ya bin koyarwar addinin Islama sau da kafa za a iya kai mai hari.

Sannan akwai wani bangare na uku kuma, wanda Mamman Annur ke jagoranta, wanda ke da kusanci da Al Barnawi wajen akida amma kuma shi da alaka da kungiyar IS.

Ta iya yuwuwa, wannan rarrabuwar kawuna da aka samu a tsakanin ‘ya’yan kungiyar, ya taimakawa dakarun Najeriya wajen rike ikon wasu yankunan da suka kwato, koda yake, rundunar dakarun hadin da aka kafa a yankin na da nata matsalolin domin Kamara yadda masu fashin baki ke fada, akwai rashin kyakyawan hadin kai a kan iyakokin da suke aiki kamar yadda aka za ta za a samu.

Sannan wata babbar barazana da dakarun ke fuskanta ita ce ta kungiyoyin ‘yan banga da aka fi sani da “Civilian JTF” wadanda suka dauki makamai domin kare unguwanninsu, inda aka samu bayanai dake nuna cewa suna cin zarafin mutane- a wasu lokuta ma har da kasha wadanda ake zargin ‘yan Boko Haram ne.

Yayin kuma da yakin na Boko Haram ke lafawa, dubban matasan da ke dauke da makamai domin kare unguwanninsu, suna neman aiki a rundunar sojin kasar da wasu hukumomin tsaro.

Kuma a cewar Zenn, gwamnati na kokarin ta ga cewa ta karbi wadannan mayaka, amma kuma saboda cimma wani burin na daban.

“Akwai damuwar da wasu ke nunawa cewa idan aka kawo karshen wannan fada, akwai yuwuwar ire-iren wadanann kungiyoyi na ‘yan banga su zama barazana ga tsaro a nan gaba – musamman ma ga su kansu.”

A yayin da duk hakan ke faruwa,  hukumomin Najeriya na ci gaba da samun nasara akan kungiyar ta Boko Haram amma ba cikin gaggawa ba.

A kwanan nan, an sake samun daya daga cikin ‘yan matan Chibok da aka sace tare da jaririnta mai watanni shida.

An gano ta ne bayan da sojoji suka yi tambayoyi ga daruruwan mutanen da aka ceto a harin da aka kai dajin Sambisa.

Ceto mutanen ya faru ne kwanaki kadan gabanin masu fafatukar neman a kubutar da ‘yan matan na Chibok suka yi taron cika kwanaki 1000 da sace ‘yan matan.

A ganin Zenn, idan aka lura da cewa har yanzu ba a ceto galibin ‘yan matan ba, wannan wata alama ce dake nuna cewa akwai sauran tafiya a kokarin da ake yi na yin galaba akan – ba kamar yadda dakarun Najeriya ke nuna cewa an kusa kawo karshen kungiyar ba.

“Idan dai har an har karbe galibin yankunan dake hanun Boko Haram kamar yadda gwamnati ke fada, ta yaya har yanzu ba a ga wadannan ‘yan matan ba?” In ji Zenn, ya na mai kara da cewa “kamata ya yi a ce an yi kicibis da wasu daga cikin wadannan ‘yan mata.”

Gano wadannan ‘yan matan –  da farfadowar ita kanta najeriya daga wannan ukuba, abu ne da za a kwashe shekaru kafin a gani.

 

DOMIN KARIN BAYANI
Kalli cikakkun faya-fayen bidiyo na “Boko Haram: Fuskokin Ta’addanci.”

ABUBUWAN DA MUTANE SUKE FADI
Bayyana mana ra'ayoyinku game da "Boko Haram: Fuskokin Ta'addanci" #terrorunmasked
Facebook
Twitter

Marubuta: Dan Joseph

Wadanda suka tsara suka gabatar Tatenda Gumbo da Steven Ferri

VOA reporters in Nigeria and Washington, D.C., contributed to this report.