A farkon shekaran da ya gabata ne wata majiya mai tushe ta sanar da wani ma’akacin Muryar Amurka cewa da ya jira wani sako daga wajensu. Bayan ‘yan kwanaki, sai ga sakon ya iso cikin wani karamin kwali, wani akwatin nade bayanai komfuta watau hard drive da aka daure da tsumma. Bidiyoyine kunshe a ciki guda 400 wadanda idan aka hada gaba daya za su kai na tsawon sa’o’i 18.
Ma’aikacinmu ya yi mamakin abun da ya fado a hannunsa bayan da ya dan kalli wasu daga cikin bidiyoyin. Mutanen dake ciki basu kasance kowa ba face mayakan Boko Haram, daya daga cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda mafi muni a duniya wadda kuma babu wata kungiyar da ta fi ta sirri. Mambobin sun kasance suna boye fuskokinsu a koda yaushe amma sai ga shi a bidiyoyin da mai daukan hotonsu ya dauka, ya nuno su su na hira, da harkokinsu na yau da kullum har da kuma yadda suke aikata ayyuka na rashin tausayi duk a fili.
Wadannan bidiyoyin ya yi karin haske sosai kan abubuwan da suka tilastawa mutane sama da miliyoyi biyu da barin garuruwansu da kauyyukansu a sanadiyyar annobar Boko Haram. Sa’annan, bidiyoyin sun bayyana mana yadda kungiyar ta zartarwa mutane hukunce-hukuncen kisa, bulala,yanke hannu,da yadda suka kaiwa wani barikin soji hari har da kuma yadda suka kashe wasu mutanen gari wajen neman kudi da abinci. Akwai wurare a bidiyoyin da ya nunosu suna aikata abubuwa kamar tsare mutanen gari don bincike,yadda suka jarraba wani karamin jirgi marar matuki wato drone, da kuma inda suka halarta jinin wadanda suka bijirewa gurbatacciyar akidarsu.
Muryar Amurka ta gano cewa lallai wadannan bidiyoyin sun fito ne daga konfutar Boko Haram da aka tsinto bayan wani samamen da sojin Najeriya ta kai musu. Majiyarta kuma ba ta da alaka da soji, gwamnatin Najeriya ko Boko Haram.
Mun sha ganin ire-iren bidiyoyin farfagandar Boko Haram amma wadannan ba a ta ganin irinsu ba. Domin ba a sarrafasu ta yadda zasu boye komai ba daga cikin ayyukansu na mugunta da rashin imani.Ga dukkan alamu, wadannan bidiyoyin an daukesu ne a karshen shekarar 2014 da 2015, lokacin da kungiyar ta yi karfi a Arewa Maso Gabashin Najeriya. Mun tsinci hakan ne daga alamomin lokaci kan bidiyoyin, da hirarsu, da kuma labaran da akeji ana watsawa a lokacin.
Muryar Amurka ta bazama wajen tantance kundin bidiyoyin inda ta kwashe watanni ta na aiki a kai har sai da ta fede biri har wutsiyansa.Mun fassara abubuwan da ke ciki, da kuma gano wuraren da aka nuno ta hotunan tauraron dan adam. Mayakan masu magana a ciki basu bayyana sunayensu ba sai dai su kira kansu da Boko Haram kuma sun fi amfani da harshen Kanuri. Ga kuma tutarsu da tambarinsu a zahiri. Daga cikin kundin, anyi amfani da akalla guda a cikin bidiyoyinsu na farfaganda da su ka yada.Sa’annan, Muryar Amurka ta je Najeriya a watan Satumbar 2016 domin ziyartar wuraren da aka nuno a ciki inda kuma ‘yan gudun hijira suka taimaka wajen gane wuraren da akayi kashe-kashe a bidiyoyin.
Wani malami a Gidauniyar Jamestown da ke Washington DC, Jacob Zenn wanda yayi nazari mai zurfi kan kungiyar Boko Haram, ya samu kallon wasu daga cikin bidiyoyin. Shi ma ya taimaka wajen gane wasu sannanu daga cikin mayakan inda ya shaida mana cewa wadannan bidiyoyin babu kamarsu wajen bayyanawa duniya yadda kungiyar ke tafiyar da harkokinta.
“Da wuya ka samu bidiyo da zai nuna maka yadda rayuwar yau da kullum ta kasance a garesu ko na yadda suke gudanar da ayyukansu wanda kuma ba na farfaganda ba,” inji Zenn. “Ya dan boko haram ya ke? Ya ya ke magana idan ba na shiri ba ne don watsa farfagandarsu a duniya?”
“Lallai kam wannan ba a taba ganin irinsa ba,” inji shi.
Tun daga lokacin da aka dauki wadannan bidiyoyin har bayan fadowarsu a hannun Muryar Amurka,rundanar sojin Najeriya tayi galaba akansu inda ta kwato garuruwa da wurare da ke hannun Boko Haram. Haka kuma, Jami’an soji da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari sun shaida cewa an fatattake kungiyar daga babban tungayensu a Dajin Sambisa. Amma har wayau, kungiyar ta na ci gaba da kaiwa soji da jama’ar gari hare-hare.
A watan Janairu, Muryar Amurka ta nunawa Ministan tsaron Najeriya, Mansur Mohammed Dan Ali wasu daga cikin bidiyoyin, ya kuma shaida cewa bai taba ganinsu ba kuma bai ma san da su ba. Amma bayan da ya kalli yadda ‘yan Boko Haram suke bugun mutane da kashesu, sai da ya yi kwalla.
Dan Ali ya ce duk da cewa gwamnatin Shugaba Buhari ta yi iya kokarinta na ganin anyi galaba akan wannan kungiya, wannan kundin bidiyoyin zai zama tuni ga duniya irin rashin imanin wannan kungiyar.
“Zai bayyana irin tsananin muguntar Boko Haram ga al’ummominmu da ‘yan Najeriya,” inji shi. “Domin wannan bala’in ko ta yaya ne, ta shafe kowa.”
DOMIN KARIN BAYANI
Kalli cikakkun faya-fayen bidiyo na “Boko Haram: Fuskokin Ta’addanci.”
ABUBUWAN DA MUTANE SUKE FADI
Bayyana mana ra'ayoyinku game da "Boko Haram: Fuskokin Ta'addanci" #terrorunmasked
Facebook
Twitter