Boko Haram: Fuskokin Ta’addanci
Barnar Da Ta’addanci Ya Haifar
Yadda Aka Hada Wannan Rahoto

BOKO HARAM

FUSKOKIN TA’ADDANCI

An fito da wani karamin yaro a fili ana masa bulala.Masu kallo sun taru suna kabbara yayin da ‘yan boko haram ke harbin mutane a kirji da kuma a kai. Abun ko a jikinsu  duk da irin ihun tuba da kin amsa laifin da suke yi.

Wannan rohoton da zai biyo zai nuna ‘yan kungiyar boko haram a fili daga wasu bidiyoyinsu da suka dauka da kansu. Muryar Amurka ta samu wadannan bidiyoyin da ka iya fusata mai kallo.

KUKUNCIN KISA

A garin Kumshe, an ga wani mutumin da aka zarga da laifin sayar da kwaya yana addu’a da kalmar Shahada jim kadan kafin ‘yan Boko Haram su kashe shi (bidiyon Boko Haram)

A wani kauye dake arewacin Najeriya mai suna Kumshe, Kungiyar Boko Haram ta zartar da hukunci kan mutane bisa mummunar fassarar da suka yi wa shari’ar musulunci.Suna yanke hukunci mai tsanani ga wadanda suka kama da laifuka kamar saka tufafi irin na turawan yamma ko don yin karatun boko da sauransu. Ana yankewa wadanda aka zarga da sayar da kayen maye hukuncin bulala ko kisa kamar yadda za’a gani a bidiyoyin.

Kalli Cikakken Kashi Na Daya Na Bidiyon Boko Haram

Ya na da wuya a samu bidiyon da ya nuno ‘Yan Boko Haram suna harkarsu a fili wanda kuma ba’a sarrafashi ba. Domin an san kungiyar da sirri sosai inda suna kokarin boye fuskokinsu don kada a gane su da kuma inda suke.

Amma duk da haka, Muryar Amurka tayi sa’ar samun fayafayan bidiyoyinsu da yawa wadanda suka nuno su a bayyane yayin da suke aikata ayyuka na rashin tausayi. Wadannan bidiyoyin da aka samo su a wata konfuta (tafi-da-gidanka?) bayan wani samamen da rundanar sojin Najeriya suka kai musu, ya shaida irin bala’in da mutane suka fuskanta a hannun kungiyar. Kalli ‘Boko Haram: Fuskokin Ta’addanci.’

Kashe-kashen da 'yan Boko Haram suka yi ya wakana ne a garin Kumshe

YADDA SUKE KAI HARI

Wani mayakin Boko Haram yana takawa ta cikin garin Banki a yayin da 'yan tsagera suka kai farmaki a kan wani barikin soja dake garin (bidiyon Boko Haram)

A shekaru bakwai da suka kwashe suna aikata ayyukan ta’addanci, Boko Haram sun kaiwa gwamnati da mutane hare-hare da niyyar tsoratar da mazauna yankin Arewacin Najeriya. Shugabannin kungiyar suna jan mutane da alkawarin zama shahidai don su turasu zuwa filin daga suyi musu yaki ba tare da makamai ko horaswa na kwarai ba. Kungiyar kuma sun sace dubban mutane musamman ma mata da yara.

Bidiyoyin da kungiyar ta dauka ya nuno wani harin da suka kaiwa wani barikin sojoji a garin Banki. An faro bidiyon ne daga sa’adda mayakan suka taru da safe tare da shugabanninsu suna shirin su je su kashe ko a kashesu. Harin dai ya yamutse inda har su mayakan suka koma ihu suna rokon a basu makami.

Kalli Cikakken Kashi Na Daya Na Bidiyon Boko Haram

Sa’annan mayakan suka kama wasu mutane daga wani kauye da ke kusa suka kashe su bayan da suka bincikesu kan abinci da kudi.

Kungiyar Boko Haram ita ke daukar nauyin kanta da kudaden da suke samowa daga yin garkuwa da mutane, ko fashi da sauransu.

TSORATARWA

'yan boko haram sun titsiye wasu yara uku su na yi musu tambayoyi jim kadan a bayan da suka kutsa cikin kauyen da yaran suke (bidiyon boko haram)

Bala’in da Kungiyar Boko Haram ta saukar a Najeriya ya lalata rayuwar mutane, da jawo tashin hankali, da kuma daidaita miliyoyin mutane a yankin arewa maso gabas.

Suna fara gudanar da bincike da zarar sun kama gari da nufin samun bayanai kan mutanen garin da ke nan da kuma na wadanda suka gudu.

Kamar yadda shugaban da ya dade yana jagorantar kungiyar ya bayyana, Abubakar Shekau, burinsu shine suyi jihadi domin su kori duk wani abu na turawan yamma daga Najeriya har sai sun kafa daularsu. Ita kungiyar babu ruwanta da sauran musulman Najeriya wajen gallazawa inda sun sha kai musu hari a masallatai ko a garuruwansu.

MAJIYA: Cibiyar Tattalin Arziki da Zaman Lafiya: Alkaluman Hare-Haren Ta'addanci Daga 2015 zuwa 2016

FAKEWA DA MUSULUNCI

'Yan Boko Haram su na shirin yanke hannayen wasu mutane biyu fararen hula da aka zarga da laifin sata (bidiyon Boko Haram)

Bidiyo na gaba ya nuno yadda shugabannin kungiyar ke gaskata kisa da sauran munanan ayyukansu kan gurbatacciyar akidarsu.

A wani kotun jama’a, wani manzo da Abubakar Shekau ya aiko ya bayyana cewa shine zai wakilci shugaban yayin da ake shirin zartar da hukuncin kisa ga wasu mutanensu biyu.

An samesu ne da laifin aikata luwadi.

Kalli Cikakken Kashi Na Daya Na Bidiyon Boko Haram

Wannan gurbatacciyar fassararsu ta addinin Islama ya samo asali ne daga koyarwar wanda ya kirkiro kungiyar, Mohammed Yusuf. Shine yayi wa’azi boko haramun ne. Yayin da rikici tsakanin kungiyar da ‘yan sanda ya munanta a shekarar 2009, ‘yan sanda suka kama mabiyansa da shi Yusuf din inda har suka kasheshi.

Shekau ya yarda da kaiwa mutane hari, sace ‘yan mata a makaranta, da kuma kashe wadanda suke kallo a zaman kafirai ko da sun kasance musulmi. A ganinsu,  jininsu ya halarci kisa tun da basu yarda da akidar kungiyar ba. Malamai da dama a Najeriya sun yi tur da mummunar akidar Boko Haram.

KOWA YA GUDU

wani gidan man da 'yan boko haram suka kona a cikin garin bama, a kusa da sansanin 'yan gudun hijira da aka kafa cikin garin (voa)

A lokacin da kungiyar ta yi tashe, wuraren da ke hannunta ya nunka girman Kasar Belgium sau biyu. Wannan ya daidaita ‘yan Najeriya sama da miliyan biyu kuma ya haddasa yanayin karancin abinci.

Garuruwa da dama wadanda ke hannunsu a da duk sun kubuta a yanzu da taimakon rundanar sojin Najeriya da na makwabata.Muryar Amurka ta samu damar ziyartar yankin a watan Satumbar 2016 don gani da idonmu ko zaman lafiya ya dawo kamar yadda ake cewa da kuma ganin sakamakon ta’addancin akan mutane.

Ayarin manyan motocin soji 18 masu manyan bindigogi ne su ka yi ma Muryar Amurka rakiya zuwa garuruwa  inda ba a iya shiga a da inda kuma muka ga yadda ‘yan Najeriya ke kokarin farfado da su. Amma ana fuskantar barazanar Boko Haram a yankunan da basu karkashin soji.

Kungiyar tana ci gaba da kai hare-haren kunar bakin wake, bindigogi da nufin mutane ko sojojin a fadin Arewa maso gabas.

MAJIYA: Hukumar Kula Da Kaurar Jama'a ta Duniya, Najeriya Disamba 2016

JUYAYIN GARIN KUMSHE

Wasu 'yan gudun hijira biyu daga garin Kumshe su na nuna jimamin ganin hotunan abubuwan da 'yan Boko Haram suka yi a garinsu. (VOA)

Wani dan gudun hijira daga garin Kumshe ya shaida mana a garinsu ne aka zartar da wadannan hukuncin kisa da bugu da muka gani a fayafayan bidiyon Boko Haram.

Ya fashe da kuka sa’adda da muka nuna masa hotunan filin da jama’a suka taru a bidiyon.

Kalli Cikakken Kashi Na Daya Na Bidiyon Boko Haram

DOMIN KARIN BAYANI
Kalli cikakkun faya-fayen bidiyo na “Boko Haram: Fuskokin Ta’addanci.”

ABUBUWAN DA MUTANE SUKE FADI
Bayyana mana ra'ayoyinku game da "Boko Haram: Fuskokin Ta'addanci" #terrorunmasked
Facebook
Twitter

Marubuta: Salem Solomon.

Wadanda suka tsara suka gabatar Tatenda Gumbo da Steven Ferri