Gabatarwa
A yayin da kasashen Turai ke ci gaba da ganin kwararar bakin hauren da aka shafe shekaru aru aru ba a ga irinta ba, labarai na mutanen dake tserewa daga yake-yake a kasashen Syria, Iraqi da Afghanistan sun mamaye kanun labarai a fadin duniya.
Amma labaran ‘yan kasashen bakar fata na Afirka wadanda ke tserewa talauci da rashin kwanciyar hankali mai tsanani a kasashensu, ba ya bazuwa a duniya, sai dai idan sun fuskanci wata mummunar ukuba a wannan hijira ta su.
Daga cikin ‘yan Afirka su kimanin dubu 130 da suka yi kokarin kaura zuwa Turai a shekarar 2015 kawai, akasarinsu su na tserewa ne daga tsananin talauci, abinda wasu suka bayyana a zaman ragowar tsarin rayuwa a zamanin mulkin mallaka.
A cikin wani sansanin ‘yan kama-wuri-zauna a birnin Rome, wani dan kasar Gambiya mai shekaru 16 da haihuwa, Morro Saneh, ya bayyana wannan hijira tasu a zaman “yunkurin yin rayuwa kamar bil Adama.”
Manyan hanyoyi biyu da dukkan ‘yan ci-rani ko bakin haure daga Afirka ke bi domin isa Turai, su kan hadu a kasar Libya, inda ake fama da mummunan tashin hankali, da kuma gwamnatoci biyun da kowaccensu ke ikirarin cewa ita ce ta halal. A nan ne ake ganin alamar wani abinda aka ce tsohon shugaban Libya, Muammar Gaddafi, ya taba fada cewa “Tekun bahar Rum, zai zamo wani wuri na rashin kwanciyar hankali.”
A nan ne bakin hauren na Afirka ke fuskantar yanayi na gaba kura baya siyaki: ga teku a gabansu, a bayansu kuma ga hamada. Shin zasu ketare teku maras tabbas mai igiyar ruwan da ka iya sauya alkibla koyaushe, wanda kuma a shekarar 2015 kawai ya lankwame rayukan bakin haure su dubu 3 da 771. Tekun da idan babu igiyar ruwa, yana ba da damar hango bakin gabar kudancin Italiya.
Amma ko da ga wadanda suka ci sa’ar kaiwa ga bakin gabar kudancin Turai din, nan da nan suke ganowa cewa Turai din fa ba kamar yadda suka zata ba ne. Kamar takwarorinsu daga kasashen Gabas ta Tsakiya, irin wadannan baki sukan kasance a gefe guda ‘yan fasa kwabrin mutane su na tatse su, a daya gefen kuma ga gwamnatocin kasashen Turai wadanda sun ki yarda su kyale su su zauna cikin kasashensu.
Ga labaransu nan.
Kashi Na Daya: Hanyoyi
A cewar Kungiyar Kula Da Kaurar Bil Adama ta Duniya, kashi 90 cikin 100 na ‘yan ci-ranin Afirka dake zuwa Turai su na bi ne ta kasar Libya; kimanin kashi 10 ta kasar Misra. ‘Yan Afirka ta Yamma, akasari daga kasashen Senegal, Gambia, Ghana da kuma Najeriya, su na isa Sabha dake Libya ta hanyar Mali da Nijar, kafin su wuce zuwa Tripoliu. Wani lokaci su na tafiyar fiye da mil dubu 10 cikin sati biyu kawai, wani lokaci kuma shekaru ma.
Daga yankin Arewa maso gabashin Afirka, ‘yan ci-ranin da akasarinsu ‘yan Eritrea ko Somaliya ne su na isa can ta kasashen Ethiopia, Kenya, Uganda da kuma Sudan ta Kudu da ta Arewa.
“Tafiya cikin Sahara ta fi tafiya cikin teku muni. A teku, mutum zai mutu, ko kuma zai rayu, amma mutum ba zai fuskanci azabar zafi da sanyi da kishi a koyaushe ba.”
– Hafsa, wata ‘yar Somaliiya a Rum
Dukkan hanyoyin su na haduwa a kasar Libya, wadda bakin gabarta ke da tazarar mil 160 daga gabar Lampedusa, watau tsibiri mafi girma daga cikin jerin tsibiran kasar Italiya da ake kira Pelagie, wanda kuma shine gabar Turai mafi kusa.
‘Yan kasashen bakar fata na Afirka ba su kai kashi 15 cikin 100 na bakin hauren da suka kwarara zuwa Turai ba, bakin haure mafi yawa da Turai ta taba gani tun bayan yakin duniya na biyu. Kusan dukkansu sun isa Turai ta kasar Italiya. Ba kamar kasar Girka makwabciyarta da ta ga tashin gwauron zabi na yawan bakin haure a saboda yake-yake a kasashen Iraqi da Syria da Afghanistan, yawan bakaken fata na Afirka dake bi ta kasar Italiya bai canja sosai ba a cikin ‘yan shekarun nan.
“Ba a samu karuwar yawan bakin haure a kasar Italiya cikin wannan shekara ba,” in ji Frederico Soda, darektan ofishin kula da ayyukan kungiyar Kula da Kaurar Bil Adama a yankin tekun Bahar Rum, mai hedkwata a birnin Rome. “Adadin wadanda muka gani yayi kama da na shekarar 2014, sai dai jinsunan mutanen suka bambanta da kuma wuraren da suka fito, watau dai yanzu an samu raguwar ‘yan kasar Syria wadanda suka fara yin kaura ta hanyar kasashen yankin Balkan. An samu karuwar ‘yan Afirka ta Yamma wadanda akasarinsu, masu gujewa talauci ne su, kuma kamar ma ana mantawa da su. Amma abin ba haka yake ba ga masu gujewa tashin hankali da fitina a yankin arewa maso gabashin Afirka.”
Kashi Na Biyu: Libya
Ga bakin haure matafiya, Libya ta zamo tamkar gaba kura baya siyaki. Da farko dai ita ce ake shiga mummunan hatsari cikin hamadar Sahara domin a kai cikinta. Sannan kuma ita ce mafarin tafiya maiu cike da hatsarin gaske na tsallake tekun Bahar Rum. Kusan dukkan matafiyan da muka yi hira da su, sun ce Libya ce zango mafi muni a tafiyarsu, amma kuma ita ce harsashin wannan tafiya, inda komai ya dogara kanta. Wannan kasa, wadda a da bakaken Afirka ke kwarara cikinta domin samun ayyukan yi, ta zamo wurin fuskantar ukuba. Wani binciken da Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar kwanan nan yayi cikakken bayani na azabtarwa, bautarwa, fyade da kuma kwacewa mutane kudade karfi da yaji da ‘yan banga, masu sumogar mutane da kuma jami’an gwamnati masu kula da gidajen wakafi na ma’aikatar harkokin cikin gida suke aikatawa.
“‘Yan Libya a bakin iyaka su na lakkada mana duka da roba, su na tilasta mana tura motocin da suka mkafe cikin yashi…su na jera mu karkashin rana mai tsanani yayin da suke cin abinci da shan ruwa a gabanmu.”
– Husein Muhidiin, Dan kasar Somaliya, a Milan
Duk da cikakken bayanin da aka tattara na cin zarafi, akasarin bakin hauren ba su san irin hatsarin da suke fuskanta ba, in ji Soda na Kungiyar Kula da Kaurar Mutrane ta Duniya. “Ba su san cewa masu fasa kwabrin mutane su na kara zamowa masu azabatrwa ba.”
Kamar yadda Sama Tounkara, dan kasar Mali mai shekaru 23 da haihuwa yake fada, “Kullum sai mutum ya gudu daga nan zuwa can a cikin Tripoli.”
Kashi Na Uku: Shaida
Wata mace mai shekaru 33 da haihuwa, mai ‘ya’ya bakwai, wadda ta haihu a wani jirgin ruwan yakin Jamus mai suna Schleswig-Holstein; wasu samari biyu ‘yan Ethiopia masu shekaru 16 da haihuwa kowannensu, wadanda ‘yan fasa kwabrin mutane suka yi garkuwa da su sai da ‘yan’uwa suka biya kudin fansar Dala dubu 8 kan kowane dayansu; wani dan Somaliya wanda ya ga mazaje su na shan fitsarinsu yayin da mutuwa ke kusantarsu a cikin hamada. Kowannensu yana da nasa labarin dabam, amma ra’ayoyin da suke cimmawa sun dogara ne a kan nasara ko rashinta wajen k,etare tekun Bahar Rum.
Shaida A Bidiyo: Rahma Abukar Ali, 33, Daga Somaliya: A lokacin da Rahma Abukar Ali ta shiga jirgin ruwan bakin haure a kasar Libya ranar 22 ga watan Agusta, ta san cewa rayuwarta ta dauki sabuwar turba, watakila mai cike da alheri, ko kuma dai tana iya rasa rayuwar tata ma baki daya a hanya.
Rahma ta shafe watanni biyar, dauke da ciki, tana kan hanya daga Somaliya zuwa bakin gabar tekun kasar Libya. Wani lokacin ta kan yi tafiya mai nisa da kafa cikin tsananin zafin hamadar Sahara. Ta kan samu sassauci kadan ne kawai idan tana barci, ko kuma idan ta samu sukunin shiga cikin motocin dake shake da mutane masu dan karen yawa dake tserewa daga yaki a arewa maso gabashin Afirka.
“JIri yana kama ni, ga gajiya sosai saboda doguwar tafiya,” in ji Rahma. A saboda ba ta son ta haihu a cikin kasar Libya, sai ta yarda ta shiga wani karamin jirgin ruwa tsoho maras kyau, duk da hatsarin yin hakan.
“Na riga na kudurta ko dai in mutu tare da dan tayin dake ciki na, ko kuma in samu nasarar kaiwa ga Turai,” in ji ta.
Sai bayan da ta haifi jaririyar da ta sanya ma suna Safiya a cikin wani jirgin ruwan yakin Jamus ne Rahma ta doshi wani sansanin ‘yan gudun hijira dake Dusseldorf. A yanzu tana jiran amsar takardarta ta neman mafaka.
“Libya zata iya zamowa Somaliyar yankin tekun Bahar Rum. Za ku ga ‘yan fashin cikin teku a Sicily, a Crete, a Lampedusa. Za ku ga miliyoyin bakin haure. Zaku yi makwabtaka da ta’addanci.”
– Saif Gadhafi, one-time heir apparent to the late Col. Moammar Gadhafi, addressing media outlets, March 7, 2011.
Shaida A Bidiyo: Sama Tounkara, 23, Mali: Sama Tounkara yana kokarin samun hutu sosai a cikin wani sansanin da kungiyar agaji ta Red Cross ta kasar Italiya ta kafa a birnin Rum, kafin ya ci gaba da tattakin da yake yi da kafa zuwa arewa.
Wannan dogon matashi daga birnin Bamako, wanda ke gujewa yaki da rashin aikin yi mai tsanani a kasar Mali, ya fara tserewa zuwa Gao a karshen daminar 2014. Daga nan sai ya tsallaka iyaka zuwa garin Tamanrasset a kasar Aljeriya. A bayan da ya shafe watanni shida yana aikin leburanci a Ghardaia, sai ya wuce zuwa Libya, inda ya taras da cewa yayi gudun gara ne ya fada zago.
“A kullum a Tripoli, mutane zasu zo da bindigogi su karbe kudadenmu,” in ji matashin. “ko kuma zasu ce mu bi su zasu ba mu wani dan karamin aiki, amma a zahiri sai suyi mana fashi.”
Wata rana cikin dare, mutane sanye da kayan sarki sun zo sun ce masa ya taimaka wajen sharar sansanin, kuma suka yi masa barazana da bindigogi, a bayan da ya nemi da a biya shi ladar yin hakan. Wannan ya sa ya yanke shawarar cewa zai gudu. A lokacin da yake tsallake tekun Bahar Rum tare da bakin haure 146 a wani dan karamin jirgin ruwa, ya dauka cewa zai mutu. A bayan awa shida a cikin teku, wani jirgin ruwan kasashen Turai ya cece su. his decision to flee. Crossing the Mediterranean aboard a small vessel packed with 146 migrants, he thought he might die. But after seven long hours on the open sea, he was rescued by a European vessel.
Shaida A Bidiyo: Dalmar da Ahmed, dukkansu ‘yan shekaru 16 da haihuwa, Ethiopia: Bayan kwashe kusan wata guda a Italiya, wadanan matasan har yanzu suna fargabar yin amfani da sunayensu na asali.
Abokanan su da ke zaune a nahiyar turai, suka kwadaita musu barin gida.
“Akwai dalilai da dama da suka sa muka bar gida,” In ji Ahmed. “Babu aikin yi, wadanda suka (kammala karatu) ma yawo kawai su ke yi a titi, hakan ya sa muka bar gida.”
Bayan sun bar Addis Ababa, sai ‘yan fasa kori suka tuka su zuwa kan iyakar Sudan mai tafiyar sa’oi takwas inda suka hadu da wasu bakin haure wadanda suke shirin fara takawa domin ratsawa cikin Sahara.
Bayan kwanaki biyar suna tafiya a wasu lokuta suna samun danin mota, sai suka isa Ajdabiya, babban birnin Gundumar Al Wahat da ke kasar Libya, mai tafiyar kilomita 150 kudu daga birnin Benghazi.
“Rana ta biyar da muka kwashe muna tfiya a rairayin Hamada, sai ruwan mu ya kare” Ahmed ya tuna. An kuma sake hada su da wasu muggan masu fasa kori, wadanda sukan azabtar da bakin hauren da suka ki sa ‘yan uwansu su biya kudaden diyya ta wayar tarho.
Tabon da ke jikin Dalmar shaida ce ga makwanni shida da ya kwashe a hannun masu fasa kori.
Shaida A Bidiyo: Morro Saneh, 16, Gambia: A wani dan karamin sansanin bakin haure, Moro Saneh ya tuna daren da ya sullube ya gudu daga gida. Ranar jajiberin sabuwar shekarar 2015 bayan wani yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba akan gwamnatin shugaba Yaya Jammeh. Shi wannan matashi ya gudu ne ba tare da sanar da iyayensa ba. Bayan da ya isa Kaolack a Senegal, sai ya biya $3,000 domin a kai shi Bamako a Mali, inda ya kwashe wata guda yana sayar da ruwa akan tituna. A birnin Agadez kuwa, ya yi aikin birkila ne, sannan a Tripoli ‘yan sanda suka kwashe ‘yan kudadensa suka kuma rufe shi na tsawon kwanaki 33.
Duk da cewa ya kudiri aniyar isa ga kasar Sweden, Saneh ya gargadi matasan Afrika da ke shirin zuwa nahiyar turai. “idan da abin a neme ni in maimaita ne, bazan sake ba, domin akwai hadurra da dama.”
Kashi Na Hudu: ‘Yan Fasa-Kwabri
A kowace shekara ana samun biliyoyin daloli daga jigilar ‘yan gudun hijira, wanda hakan ke kara fadada ayyukan gungun masu manyan laifuka da ke samun riba. Sukan dai yi amfani na burin na bakin haure na zuwa turai domin sanin hanyar da suka yi na da muhimmanci ga bakin haure lamarin da suke amfani da shi domin cutar su.
Daga Khartoum zuwa Calais, labaran cin zarafi ne ke fitowa kuma masu kama da juna: masu fasa kori suna azabtar da bakin haure a rairayin Hamada, suna kashe tabar sigari a kansu ko hannayensu ko kuma a kirjinsu. Suna maida mutane kamar dabbobi ta hanyar saka su a cikin motocin da ke ratsa Hamada. A wasu lokuta sukan rufe su a kurkuku inda sukan nemi a biyasu kudaden diyya a Libya.
“A wasu lokuta, Magafe (yadda ake kiran ‘yan fasa kwabri a Somaliyanci) ba su ba mu itace ko gawayi na dafa abinci. ..Na ga masu dafa mana abinci su na kona takalma ko rigunanmu don kada yunwa ta kashe mu.”
– Hafsa, wata ‘yar Somaliya a birnin Rum
Ko a kasar Italiya, masu fasa korin jama’a su kan yi harkokinsu ne a fili. Wani dan Eritrea ya gayawa VOA cewa an gargade shi da kada ya yi rijista da jami’a yayin da ake rrike da wasu a wani gida da ke Catania har na tsawon kwanaki 10. An sake su ne bayan da aka biya dubban kudade a matsayin kudin fansa.
Wadanda suke da damar ci gaba da tafiyar sukan samu wasu haramtattun hanyoyin inda sukan sami wasu dake musu jagora har su tsallaka tekun Bahar Rum zuwa hamshakan iyayen gijin masu aikata laifukka na Albania da ke aiki a sansanonin a arewacin Faransa. A wasu lokuta akan sami wadanda basu da ko sisi sukan daukin alkawarin biya idan suka isa suka fara aiki.
A cewar Giovanni Abbate,na kungiyar IOM, ‘yan mata sukan shiga harkokin karuwanci domin biyan ubannin gidansu.
Kashi Na Biyar: A Karshe
Hare-haren ‘yan kungiyar Al shebab na daga cikin abinda ya sa Nimco Muse Ahmed ta fice daga gida. Ta na da ‘ya’ya biyu ta kuma wuce wuraren da ake yaki da kuma tsallaka teku akan wani abu mai kama da kwalekwale.
Bayan ta isa birnin Vienna, garin da ake mai kallon “Aljannar Duniya” ganin cewa Majalisar Dinkin Duniya ta saka shi a farkon jerin sunayen garuruwan da ake samun walwalar rayuwa. Anan ne ta fado daga saman wani bene dake barikin soji zuwa kasa.
“Na fita daga hayyaci na dan wani tsawon lokaci, na karya kafafuna da kashin bayana” in ji Ahmed wacce ta ba da bayanin yadda ta yi kokarin kashe kanta a wani sansani da hukumomin Austria suka kafa a Traiskirschen, wata tsohuwar makaranta da ke wajen birnin kasar.
Ta shiga halin kunci bayan da ta samu labarin cewa an ki amincewa da takardun da ta mika domin neman mafaka. A daidai lokacin da take tunanin yin watsi da lamarin sai wata satar waya da aka yi ta haddasa fada tsakanin bakin hauren Somaliya da Syria, har abin ya kaita makura.
“Na shiga halin kunci matuka bayan da naga cewa ba a amince da ni ba” in jita. “Ya kamata mutanen Afrika musamman ‘yan Somaliya su gane cewa babu wani abu a nahiyar turai, saboda haka kada ma su yi mafarkin zuwa.”
“A yanzu kam na ga zahiri. Dusar kankara. A lokacin da nake Afirka ba na fuskantar yunwa. A nan kam, yunwa nake fuskanta.”
– Nimco Muse Ahmed, dan gudun hijirar Somaliya a kasar Austriya
Ya kan yi wuya ya kasance darasi ga mafi yawan bakin haure daga dake tunkarar nahiyar turai, amma wani abu a labarin Ahmed ya nuna karara irin bakar wuyar da suke fuskanta.
Kamar mafi yawan ‘yan gudun hijra da yawansu ya kai miliyan daya suka isa turai a shekarar 2015 kadai, kokarin samun ingantacciyar rayuwa na nufin za ta bar iyalanta, wadanda ta karbe dan kudaden da ke hannunsu domin tunkarar rayuwa ko mutuwa akan teku, lamarin da ya sa ta tsinci kanta babu gida babu paspo babu jiha- a arewacin wata nahiya.
Ba kamar ‘yan kasar Syria da na Afghanistan da Iraqi ba, wadanda su suka mamaye mafi yawan masu isa kasar, Ahmed ta ce wadanda suka fito daga yankin Afrika yamma da sahara suna fuskantar wariya ta daban.
A duk wuraren da suka je a nahiyar, abokan tafiyarsu da suka fito daga yankin Larabawa da Afghanistan sukan mai da su saniyar ware.
Matsalar da aka samu ta satar wayar hannu ta sa mutanen a cikinj tsaka-mai wuya domin abokananmu na Afgahnistan da suke da ilimi sun yi saurin wanke kansu fiye da yawa daga cikin mutanenmu da wadanda aka daura alhakin satar wayar.
Wuraren da Bakin Haure Daga Kudancin Hamada ke Nufa
TSARI MARA TASIRI
Ga ‘yan gudun hijra irinsu Ahmed, babu wata mafita mai sauki, Yayin da kungiyar kasashen nahiyar turai mai mambobi 28 ke fama da kwararar ‘yan gudun hijra da tabarbarewar tattalin arzikin Girka da kuma jerin hare-hare, babu wata alama ta hadin kai tsakanin ‘ya’yan kungiyar wajen neman maslahar wadannan matsaloli. Wata kididdiga da aka yi kan tattalin arzikin nahiyar ta nuna karin ‘yan gudun hijra miliyan uku a shekara mai zuwa. Sannan Burtaniya, daya daga cikin manyan kasashen nahiyar, na shirin gudanar da zaben jin ra’ayin jama’a kan yunkurin ta ficewa daga kungiyar. Ana ma wannan lamarin kallon abin da ka iya girgiza nahiyar.
Hukumomin nahiyar ta turai basu da takamaiman tsari na shawo kan wannan matsala, duk da cewa sun yi alkawarin rarraba masu neman mafaka dubu 160,000 da aka tantance a tsakanin kasashen kungiyar. Ya zuwa ranar 12 ga watan Disamba, an tsugunar da mutane 159. Kasar Canada ta yi maraba da wasu ‘yangudun hijra su dubu 25,000 da suka fito daga Syria a ranar 11 ga watan Disamba.
Yayin da ‘yan majalisar dokokin Amurka ke shirin gudanar da muhawara ta biyu kan shirin Shugaba Barack Obama na baiwa masu nemana mafaka dubu 10,000 daga Syria matsuguni, batun shigar baki kasar ta Amurka, ya kasance babban batu a zaben dake tunkarar kasar, inda mai neman takarar shugabancin kasar daga Jam’iyyar Republican Donald Trump ya sha alwashin saka tsaurara matakan tsaro ga musulmai masu buri shiga kasar tare da maida duk wani dan kasar Syria da ya samu mafaka a karkashin shirin Obama. Duk da hobbasar da Fadar White House ta yi na shirin shigar baki kasar, kokarin baiwa wasu tafinta a filin yaki ‘yan kasar Afghanistan da Iraqi vizar shiga kasar ya ci tura.
Amma yayin da kasashen nahiyar turai a gashin kansu ke nazarin takardun masu neman mafaka, kula da ‘yan gudun hijra da ke isa Italiya da Girka ya kusan komawa hannun kungiyoyin ba da agaji da masu aikin sa kai da kananan hukumomi.
“Akwai miliyoyin bakar fata da zasu iya tahowa nan bakin gabar tekun Bahar Rum domin su tsallaka zuwa Faransa da Italiya. Libya tana taka rawa wajen tabbatar da tsaro a yankin tekun Bahar Rum.”
– Moammar Gaddafi a lokacin da yake magana da gidan telebijin na France 24 a watan Maris na 2011.
“Menene ya sa watanni bayan fuskantar wannan matsala, masu ayyukan sa kai ne kadai ke kawo gudunmuwa ga masu isa turai?” In ji Peter N. Boucket, darekta a kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch a wani rubutu da ya yi a kwanan nan a Girka. “Menene ya sa masu ayyukan sa kai ne kadai ke ba da magunguna a yankin Lesbos ba tare da motocin daukan marasa lafiya ba daga gwamnati ko kuma wasu ma’aikatun gwamnati?” in ji shi.
Wasu rahotanni da dama a kafofin labarai su ma sun kara amon wannan sukar lamiri, su na bayyana cewa da wuya kaga wakilan kungiyar nahiyar turai a gaba-gaba wajen taimakawa.
“Border management is primarily a responsibility of the national authorities,” a European Commission spokesperson said via email. “The European Commission and EU Agencies help and support member states and national authorities managing the situation on the ground — but they do not replace member states.”
Sai dai a bangare guda kuma, kungiyar ta EU ta fara wani shiri na lalubo dalilan da ke sa jama’ar Afrika ke ficewa. A wani taro da aka yi a watan Nuwamban bara kan matsalar kwararar ‘yan gudun hijrar, shugabannin EU da na kungiyar kasashen Afrika sun saka hanu a wata yarjejeniyar samar da dala biliyan 1.9 domin gudanar da ayyukan mayar da ‘yan Afrika zuwa kasashensu. Kasar Malta wacce ta karbi bakuncin taron da kuma kasancewa daya daga cikin masu fama da ‘yan gudun hijrar, ta yi alkawarin ba da dala dubu 270.
Wata guda bayan haka, jami’an kungiyar ta EU sun kaddamar da wani shirin tallafin dala biliyan biyu domin dakile yawaitar kwararar ‘yan Afrika zuwa turai saboda rashin ayyukan yi da kuma taimakawa sauran kasashen da ke haifar da kwararar ‘yan gudjn hijra.
Matakan dakile kwararar ‘yan gudun hijra ta hanyar tekun Bahrarrum sun kasance a kasa tun kafin kifar da gwamnatin Gaddafi. A shekarar 2011, ministan harkokin wajen Italiya a wancan lokacin. Franco Frattini ya yi kira da a samar da wani sabon tsari a yankin.
“Ya kamata Kungiyar EU, da sauran manyan hukumomin duniya kamar su Babban Bankin Duniya da hukumar ba da lamuni ta IMF, su samar da wani shiri dai zai kula da tattalin arzikin yankin tekun Bahrurrum.” In ji Frattini a cikin wani sharhin da ya rubuta a jaridar Financial Times a 2011,yana mai nuna misali da shirin da Amurka ta yi na farfado da yammacin Turai bayan yakin duniya na biyu. “Wannan shiri ya tattaro masu fada a ji a fannin tattalin arzikin nahiyar turai da sauran ma’aikatun kudi na duniya, ta hanyar ware biliyoyin kudaden euro domin a kayata yankin da gayyato masu saka hannun jari.”
Frattini ya kuma yi kira ga jami’an nahiyar turai da su cire takunkuman da ke tsakanin kasashen da ke yankin Bahrurrum da sauran kasashe su kuma yi aiki kafada da kafada da Amurka “wacce ta ke da muhimmiyar rawar da za ta taka.” Sannan ya kwadaitar kan bukatar samar da ilimi domin inganta rayuwar matasa wanda hakan zai kawar musu da kwadayin shiga kungiyoyin ‘yan ta’adda. Haka kuma ya kira da a samar da wani tsarin musayar ilimi a bangarorin kasashen da ke gefen tekun Bahrurrum da ta hanyar horar da matsa ayyuka wanda ya ce “tsarin shi ne mafita mai inganci wajen dakile kwararar bakin haure da safararsu.”
Masu fashin baki a fannin kwararar bakin haure sun ce ba za a iya kawar da wannan matsala ba ta hanyar dakile matsalolin daga bangaren abubuwan da ke haifar da gudun hijra daga Afrika.
“Laifin nahiyar Turai anan shi ne gazawar da ta yi na zuwa kawo dauki”, Heins de Haas, wani Malami a fannin nazarin halayyar dan adam a Jami’ar Armsterdam, ya gayawa jaridar The Huffington Post. Yayin da ‘yan gudun hijrar daga yankunan da ake yake-yake da masu neman mafakar siyasa ke tunkarar turai, wadanda suke samun kariya daga Majalisar Dinkin Duniya, tattalin arzikin nahiyar turai da ke ci gaba da lale ga kowa, zai neman masu aiki cikin farashi ma rahusa amma sai dai dokokin shige da ficen da aka gindaya ba su yi hanun riga da abin da ke kasa, a cewarsa.
Ya ce “Mutane sun gane cewa yanzu babu wannan kariya da nahiyar turai ta ta kasance ta na da ita shekaru 25 da suka gabata.” Hakan kuma ya sa ake samun safarar mutane da wahalar da ‘yan gudun hijra ke fuskanta da kuma yawaitar mace-mace.
Amma saboda akwai kyakyawar alaka tsakanin burin masu shiga nahiyar da kuma dokokin shige da ficen da hadahadar kasuwancin turai, Elizabeth Collet, darekta a wata cibiyar nazarin yin kaura a Brussels, ta ba da shawara a maida hankali kan kananan shirye-shiryen tsara ko kuma bunkasa tattalin arzikin wasu yankunan.
Ta kara da cewa “manyan tsare-tsaren ci gaba ba za su iya dakile matsalar yin kaura ba.” “sai dai akwai wasu abubuwa takamaimai da wadandan ba lallai ba ne su zamanto za su dakile tafiye-tafiye, amma kuma wadanda suke kokarin samar da dama da za ta hana mutane su jefa rayuwarsu cikin hadari inda daga karshe ba za a cimma buri ba.”
Watakila tambayar anan ita ce, shin ko kungiyar tarayyar turai ta EU ta maida hankali kan maye gurbin tsarin da Gaddafi ya samar, kananan ma’aikatu da za su samar da ayyukan yi wadanda za su baiwa mutane irinsu Nimco Muse Ahmed wata mafita da za su koma rayuwarsu ta da, ba tare da ta yi kokarin sauya wata rayuwa a nahiyar turai ba?
Ba Gudu, Ba Ja Da Baya
Sai dai samar da daidadaito na dan wani lokaci, ka iya zama maras tasiri bayan kifar da Gaddafi a Libya wacce kan iyakokinta da ke wangale ya haifar da masu adawa da kwararar bakin haure a kasashen nahiyar turai. Yayin da masu tsare-tsare suka dukufa wajen nemo bakin zaren wannan matsala, ta iya yuwuwa maslahar wannan matsala ba a birnin Brussels ta ke ba, ta iya kasancewa ta na duk inda aka tilastawa mutane ficewa daga muhallansu, wanda hakan shi ke kai mutane da dama ga bin wannan tafarki mai cike da hadari.
Peter Cobus ya taimaka da bada rahoto daga Washington, DC.
Wadanda Suka Shirya
Rahoton Abdulaziz Osman da Nicolas Pinault.
Edita Peter Cobus.
Tsarawa don yanar gizo: Stephen Mekosh da Dino Beslagic.
Mai Kula Da Wannan Aiki: Steven Ferri.
Masu Sarrafa Abubuwan Cikin rahoton: Teffera G. Teffera da Ezra Fessahaye.
Sharhi