Fadawa Cikin Tarkon Ta'addanci

Yadda wani matashi Baturke ya rikide daga masanin taurari ya koma mayakin kungiyar Da’esh

Rasid Tugral ya samu masoya da yawa a shafukan sada zumunci na intanet a saboda hotuna masu ban sha’awa da ban mamaki da ya rika sanyawa na taurari da abubuwan dake cikin samaniya, wadanda ya dauka a kasarsa ta haihuwa, Turkiyya. Ya wallafa hotuna da dama, kamar wannan hoto na wata bishiyar da ya dauka yana hangen tsakiyar falakin da duniyarmu ke ciki, wadda ake kira Milky Way Galaxy a turance, a wani shafin mujallar National Geographic. Ya shiga wata jami’a domin karatun babban digirin da ake karramawa kan nazarin sigar taurari da samaniya a kasar Finland. An ga alamun cewa Rasid, mai basira da kwakwalwa, kyakkyawa da shi, kuma mai son jama’a, zai yi fice a fannin nazarin taurari da samaniya.

Amma kuma, akwai abubuwa da Tugral yake kwadayi a rayuwarsa. A lokacin da yake jami’a, Tugral, wanda Musulmi ne mai son addini, kuma ya fito daga gidan da ake kula da addini sosai, ya fara kashe lokaci yana duba shafukan ‘yan jihadi a kan intanet. Tugral ya rungumi yadda suke fassara addini cikin akida ta tsageranci. A farkon shekarar 2015, ya gudu daga gidan iyayensa, yayi watsi da rayuwar jin dadi, ya shiga sahun mayakan Da’esh, ko Daular Islama, dake yaki a kasar Sham (Syria).

Ya zuwa watan Agusta da ta shige, Tugral yam utu, bisa dukkan alamu a lokacin da yake yaki ma kungiyar Da’esh a awata karawa da sojojin Kurdawa. Ya bar duniya yana da shekara 27 da haihuwa.

Dubban matasa Musulmi sun yi tattaki domin yaki ma daular da ‘yan ta’addar suka ayyana kafawa a Iraqi da Sham, a dalilin rungumar akida da kuma farfagandar Da’esh. Kamar Tugral, da yawa daga cikin irin wadannan matasan su kan yi watsi da Rayuwa ta jin dadi ne. Sai dai shi labarinsa ya fito fili ne a saboda rubuce-rubuce da hotunan da yayi ta wallafawa cikin shekaru goma, inda yayi ta bayanin rikidewar rayuwarsa zuwa ga dan ta’adda.

Tugral ya dauki hoton da ya hango tsakiyar falakin da duniyarmu ke ciki, wadda ake kira Milky Way Galaxy a turance. Ya dauki hoton ne daga Cibiyar Nazarin Samaniya ta Kasa ta TUBITAK a Turkiya. 7 ga watan Oktobar 2014.

Tugral ya dauki hoton da ya hango tsakiyar falakin da duniyarmu ke ciki, wadda ake kira Milky Way Galaxy a turance. Ya dauki hoton ne daga Cibiyar Nazarin Samaniya ta Kasa ta TUBITAK a Turkiya. 7 ga watan Oktobar 2014.

A cikin shekarun da yayi yana wallafe-wallafe, ya bar ma duniya gadon hotunan da ya dauka na kansa, da na kyanwoyi da yayi sha’awa a rayuwarsa; da kalamai kan sararin samaniya da addininsa; da kuma bakaken maganganu kan wadanda ba Musulmi ba. A cikin wata doguwar wasikar da ya wallafa a intanet a shekarar da ta shige, yayi bayanin dalla-dallar yadda Rayuwa take gudana tare da Da’esh: zaman kashe wando; horaswa mai tsanani ta koyon aikin soja, da kuma kaucewa bama-baman da ake cillo musu daga sama. A cikin wani yanayi na nuna cewa akidarsa ta fi ta kowa, ya fito yana kare abubuwa mafiya muni da ‘yan Da’esh suke aikatawa, ciki har da sare kan mutane da bautar da mata domin yin lalata da su.

Wani lokacin, ya taba rubutawa a shafinsa na Facebook cewa, “Duk wanda ya mutu bai yi yaki a Jihadi ba, to ya mutu a matsayin munafuki” yana mai kafa hujja da wani hadisi. Sai dai malamai da dama, kamar Khalifa Aliyu Ahmad Abul Fathi da Sheikh Ibrahim Muhammad Duguri, sun ce ‘yan tsagera suna juya zahirin ma’anonin Musulunci, da ma’anar Jihadi, kuma addinin Musulunci yana yin tur da ta’addanci da kai hare-hare a kan fararen hula wadanda ba mayaka ne a bakin dag aba.

Me ya ja hankalin Tugral ya rungumi tsageranci da ta’addanci? Wasu wakilan VOA sun nemi amsoshin wannan ta hanyar bitar abubuwan da Tugral ya wallafa a shafukan sada zumunci na intanet, da wasika mai shafi 14 da ya rubuta a farkon zuwansa kasar Sham, suka fassara ta daga harshen Turkanci. Hari la yau sun yi hira da wasu abokan matashin, da kuma wasu majiyoyin ciki har da wata ‘yar gajeruwar hira da mahaifinsa.

Tugral bai faro ta hanyar jihadi ba, kuma ba hanya ce da aka zaci zai runguma ba a saboda basirarsa da kuma son mutane da barkwanci. Rayuwarsa da mutuwarsa sun nuna irin yadda Musulmi matasa na wannan zamani da suka bata a hanya, suke rungumar akida maras tushe da rayuwar karya ta ‘yan Da’esh.

Ya Tashi A Gidan Da Aka Rike Addini

Tugral shine na biyu cikin yara ukun da iyayensa suka haifa. Iyayensa masu son ilmi da addini ne sosai. Mahaifinsa yana da digirin PhD a Adabin Turkawa, yana kuma koyarwa a wata makarantar sakandare. Yayansa injiniya ne na manhajar sarrafa na’urorin kwamfuta (software), sannan yana rubuta wakoki; kanwarsa daliba ce, sannan yana da wani kawu ta wajen uba wanda shaihin malamin lissafi ne.

Mahaifinsa, Suleyman Tugral, yayi rubuce-rubuce kan addinin Islama daga 2008 zuwa 2014, inda ya rika wallafa wakoki da akidarsa ta ra’ayin ‘yan mazan jiya. Hari la yau, ya wallafa maqalar da ya rubuta ta samun babban digirinsa na PhD a kan “Tsarin Tarbiyya Cikin al-Qur’ani” inda ya bayyana goyon baya ga jihadi da makami, tare da bayyana Yahudawa da Kiristoci a zaman la’anannu a saboda basu yi Imani da Allah da AnnabinSa ba. “Azaba mai radadi tana jiransu” a yadda ya rubuta.

A lokacin da Rasid yake makarantar sakandare, Suleyman da matarsa sun sanya dan nasu yana karatun Qur’ani a gida, abinda aka saba gani a gidajen da suke rike addini sosai.

A sama: Hoton da Tugral ya dauka a Cibiyar Nazarin Samaniya ta Kasa ta TUBITAK inda ya hango tsakiyar falakin da duniyarmu ke ciki wato Milky Way da kuma tsayuwar wata. Yasa hoton a intanet ranar 14 ga watan Oktobar 2014.Tare da: Hoton da aka dauka daga jirgin sama, yayin wani bikin taurari da akayi a 2012 a cibiyar nazarin sararin samaniya ta kasa dake TÜBİTAK Antalya, Turkiya. Yasa hoton a intanet ranar 12 ga watan Oktobar 2014.

A sama: Hoton da Tugral ya dauka a Cibiyar Nazarin Samaniya ta Kasa ta TUBITAK inda ya hango tsakiyar falakin da duniyarmu ke ciki wato Milky Way da kuma tsayuwar wata. Yasa hoton a intanet ranar 14 ga watan Oktobar 2014.


Tare da: Hoton da aka dauka daga jirgin sama, yayin wani bikin taurari da akayi a 2012 a cibiyar nazarin sararin samaniya ta kasa dake TÜBİTAK Antalya, Turkiya. Yasa hoton a intanet ranar 12 ga watan Oktobar 2014.

Akwai Shi Da Basira, Amma Ba Ladabi

A karshen shekarar 2007, Rasid Tugral ya shiga Jami’ar Kimiyya ta Gabas ta Tsakiya, METU a takaice, wadda ake mata lakani da sunan Jami’ar Harvard ta Turkiyya, domin yayi nazarin Kimiyyar Sigar Samaniya da kasa da duk abubuwan dake tsakaninsu, watau Physics a turance. Daya daga cikin tsoffin dan ajinsu a jami’ar, Nihat Celik, wanda yana daya daga cikin wadanda suka tabbatar da sahihancin rubuce-rubucen Tugral da hotunansa a shafukan sada zumunci na intanet, yace tsarin zaman makaranta, inda ba a kula da addini ba, ya sha bambam sosai ma Tugral wanda ya saba da Rayuwa ta addini a gida.

“Da rana yana zuwa makaranta a yanayi na zaman rayuwar da ba ta addini ba. Da daddare kuma, yana gida inda ake bin dokokin addini sosai tare da iyaye da ‘yan’uwansa,” in ji Celik. “Ba ta yiwuwa mutum ya hada irin wadannan tsare-tsaren Rayuwa guda biyu a wuri guda.”

A wannan hoton da ba’a san lokacin da aka dauka ba, Tugral yana yawon shakatawa a Antalya, Turkiyya.

A wannan hoton da ba’a san lokacin da aka dauka ba, Tugral yana yawon shakatawa a Antalya, Turkiyya.

A Jami’ar METU, Tugral yayi suna a saboda sha’awar da ya nuna kan binciken sararin samaniya da daukar hoto, da kuma barkwancin da yake yi a wasu lokuta. Wani shaihin malami, wand aba ya son a ambaci sunansa a saboda tsaro, ya ce Tugral “mai matukar basira ne. Yana yin tambayoyi masu ma’ana sosai. Sai dai ba shi da ladabi, wasu lokutan bay a zuwa aji.”
Tugral ya shiga cikin kulob na masu nazarin taurari da samaniya na Jami’ar, har ya zamo abokin shugaban kulob din, Utku Boratac. Su kan tafi yawo cikin daji tare inda suke nazarin taurari da samaniya. Boratac ya fadawa VOA cewa sun kuma taimaka wajen shirya taron shekara da aka saba yi na kallon taurari na Cibiyar Nazarin Samaniya ta Kasa ta TUBITAK.
A shekarar 2010, Tugral ya fara wallafa hotunan taurari da samaniya da yak dauka a wani shafin membobin kungiyar nan ta National Geographic sannan kuma a shekara ta 2012 ya shiga wata gasar da Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Amurka, NASA, ta shirya ta harhada hotuna daga madubin hangen samaniya na Hubble. Shafukan sada zumunci na intanet, ana kiransa da sunan Nukleer Kedi, watau Kyanwar Nukiliya a Hausance, a saboda yadda yake sha’awar kyanwa da kuma irin hotunansu da yake wallafawa a intanet.

Tugral ya sa wannan hoton a Facebook ranar 8 ga watan Oktobar 2014 inda ya rubuta, “Ina karatu amma bacci na son dauka na.”

Tugral ya sa wannan hoton a Facebook ranar 8 ga watan Oktobar 2014 inda ya rubuta, “Ina karatu amma bacci na son dauka na.”

Mai Ra’ayin Kansa

Wani mutumin da suka yi karatu da Tugral, amma bay a son a bayyana sunansa domin ba ya son a alakanta shi da mutumin, yace Tugral mutum ne mai son wasa da yin barkwanci game da komai, da bayar da labarai na ban dariya. Yace akwai lokacin da yazo makaranta sanye da wando irin mai kama jiki sosai, wata rana kuma sai suka gan shi da gajeren wando babu riga a jikinsa.

Tugral, mutum ne mai son motsa jiki ta hanyar hawan keke, da tattaki da kuma ninkaya. Dan ajin nasu, ya tuno da cewa “watarana, ya rasa abin yi, saboda haka yah au keke ya tuko tun daga Ankara (babban birnin Turkiyya), har zuwa Konya (a kudancin kasar),” tafiyar kilomita 262, ko mil 163.

Nan sama: Wani bidiyon kulob na masu nazarin taurari da samaniya na Jami’ar da akayi a 2009, inda ya nuna mambobinl suna bayyana yadda duniya take, An nuna Tugral a ciki.

“Yawancin mutanen da na sani, su na ganin kamar ba ni da hankali, , amma kuma su na sha’awar su zamo kamar ni a saboda ina yin duk abinda na ga dama. Daya daga cikin abubuwan shine yawo kan keke,” in ji Tugral a cikin wani rubutun da yayi a shafin wani kamfanin dake da gidajen baki mai suna Couchsurfing a intanet.

“Ni mai son dariya ne, tare da sanya mutane su yi dariya (koda yake wani lokacin na kan yi kuka). A yawancin lokuta, mutanen dake kusa da ni ba su zaman bacin rai idan ina kusa da su.”

Gusawa Ga Tsageranci

A Jami’ar METU, Tugral ya ci gaba da kasancewa mai rike addini, amma kuma yana yin hulda da mutanen da su kam ba su damu da yin salloli, ko azumi ba, sannan su na shaye-shaye.

“Akwai watarana muna shan barasa,” in ji wani abokin nasa wanda y ace kada a fadi sunansa domin yana tsoron ‘yan tsagera zasu iya far masa. Tugral “bai zauna ya sha giya tare da mu ba, amma kuma yayi ta zolayar kansa a kan cewa me yasa ne shi ba ya sha.”

A shekarar 2013, ya shiga cikin zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati, ya kuma fara kara kusanta kansa ga addininsa. Boratac yace sun ga Tugral ya fara sauyawa.

Da kadan da kadan, Tugral ya fara janyewa daga sauran daliban jami’ar METU wadanda bas u damu da addini ba. Kamar yadda al’adar ‘yan Daesh take, ya ajiye gemu ya kuma daina aske gashinsa. A shafinsa na Facebook, yayi ta sukar lamirin yadda “’yan kwaminis na METU suke taruwa nan take su na yi maka dariya idan ka gaida ‘yan’uwanka ta hanyar hada goshi da goshi.”

Masu Ibada yayin da suke jiran abincin bude baki bayan sallar Magriba a masallacin Jami’ar METU a ranar 22 ga watan Fabrairun 2015. (Mun samu hoton ne daga al’ummar masallacin METU)Tugral ya dauki hoton Cibiyar Nazarin Samaniya ta Kasa ta TUBITAK, yadda ya nuno sama cike da taurari a Antalya, Turkiyya. Ya sa hoton a intanet ranar 26 ga watan Oktobar 2014.


Masu Ibada yayin da suke jiran abincin bude baki bayan sallar Magriba a masallacin Jami’ar METU a ranar 22 ga watan Fabrairun 2015. (Mun samu hoton ne daga al’ummar masallacin METU)

Tugral ya dauki hoton Cibiyar Nazarin Samaniya ta Kasa ta TUBITAK, yadda ya nuno sama cike da taurari a Antalya, Turkiyya. Ya sa hoton a intanet ranar 26 ga watan Oktobar 2014.

A wannan lokacin sai ya fara zama tare da yin hulda da wadanda ke taruwa a masallacin Jami’ar, inda Boratac yace yak an shafe tsawon awoyi yana tattaunawa kan ayoyin Qur’ani. “Wani lokaci yayi rubutu kan shafinsa na Facebook game da Islama. Nayi kokarin yin sharhi ko zai amsa mini. Ko kala bai ce ba.”

Celik, wanda shi ma yana cikin kulob din nazarin taurari da samaniya na Jami’ar, ya fadawa VOA cewa a wani lokaci, Tugral ya kan yi kwana da kwanaki, ko ma makonni da dama, yana zaune cikin masallaci yana nazarin Qur’ani. Yace wani abinda ya janyo abokin nasa ya zamo dan tsagera shine shigar da yayi cikin wata kungiyar nazari ko karatu a masallacin. Celik yace ya zuwa farko farkon daminar 2014, “mutum guda daga cikin ‘yan wannan kungiya ya tafi Sham ko Iraqi. Ba mu san abinda ya same shi ba.”

A cikin wani rahoton da ta rubuta a shekarar 2015 kan yadda tsagera suke samun sojojin haya har ta yi magana kan Tugral, mujallar Newsweek ta ce wani tsohon memba na wannan kungiyar karatu a masallacin jami’ar ya shiga Daesh kuma yana musanyar bidiyo na ‘yan ta’adda da shi a kan intanet. Rahoton yace ba a cika mayarda hankali a kan Turkawa masu goyon bayan Daesh ba a yayin da gwamnatin Turkiyya ke mayarda hankali ga mayaka ‘yan kasashen waje dake tsallaka bakin iyakarta da Sham.

Akai akai Tugral ya kan jagoranci salloli a masallacin jami’ar saboda baiwar da Allah ya masa na iya magana, kamar yadda wani mai bincike a fannin Physics na Jami’ar METU da yayi karatu tare da shi, Ufuk Tastan ya shaidawa jaridar BirGun na Turkiyya.

Ba da jimawa ba, Tugral ya fara bayyana goyon bayansa ga yin jihadi. A shafinsa na Facebook, ya bayyana bakin cikinsa game da mutuwar fararen hula a dalilin hare-haren sama da Syria, Rasha. Ya kuma yi watsi da kasarsa ta Turkiyya.

Karatu a Kasar Finland

Tugral ya kammala karatunsa a Jami’ar METU a daminar shekarar 2014. Da shigowar kaka, sai ya samu damar fara karatun digiri na biyu a fannin kididdigar kimiyya ta Physics a Jami’ar Jyvaskyla da ke Kasar Finland. Ya kuma gamsu da yadda yanayin kasar ya ke kamar yadda ya shaida a shafinsa na Facebook inda ya ke cewa, “Tabbas wannan jami’ar da nake yanzu, ta fi wacce na gama.”

Ya saka hotuna a kofofin sadarwa yana mamakin yadda ko’ina ya kan rikida da kaka. Inda za ka ga ganyayyaki sun sauya daga kore zuwa ruwan dorawa. Ya kuma saka hotunan dabbobi daban daban kamar su irin kyanwa, kurege, da sauransu.

Hoton da ya dauka a wani kauye mai kayatarwa, Äkäslompolo dake yankin Kolari a Finland. Wannan hoto ya sa shi a intanet ranar 26 ga watan Disambar 2014.Ya dauki hoton wani nau’in haske da ke haskaka samaniya da launuka dabam-dabam da akewa lakabi da Hasken Arewa ko Aurora Borealis. Hoton da ya sa  a shafinsa na Facebook ranar 27 ga watan 2014.


Hoton da ya dauka a wani kauye mai kayatarwa, Äkäslompolo dake yankin Kolari a Finland. Wannan hoto ya sa shi a intanet ranar 26 ga watan Disambar 2014.

Ya dauki hoton wani nau’in haske da ke haskaka samaniya da launuka dabam-dabam da akewa lakabi da Hasken Arewa ko Aurora Borealis. Hoton da ya sa a shafinsa na Facebook ranar 27 ga watan 2014.

A lokacin sai ya zamo bai damu da karatun da ya kai shi kasar ba, hankalinsa gaba daya sai ya koma zuwa Masallacin An-Nur da ke garin Jyvaskyla.

“Ba ya zuwa aji, sai dai ya je masallaci ko kuma ya hau kan yanar gizo a duk lokacin da ya shigo gida”, inji wani da suka yi zama tare a gida daya, Anbu Posakkannu, a tattaunawarsu da jaridar Birgun ta kasar Turkiyya.

“Tugral ya dade da bayyana sha’awarsa ta shiga kungiyar Daesh,” inji Posakkannu. Muryar Amurka ta yi kokarin samun karin bayani gurinsa amma hakan bai yiwu ba.

A tattaunarwar Muryar Amurka da abokinsa na Jami’ar METU, Boratac, ya ce ya na iya tunowa wani lokacin da ya ke zolayar gemun Tugral, har yace da shi, “Ina mamakin yadda su ka amince ka shiga Finland da irin wannan shiga, shin ba su tambayeka ko jihadi zaka je ba?” Sai yace, “ai kamannin mutum bai damesu ba illa niyyar da ya zo da ita!”

Sai dai daga baya aka zo aka fara shakkar niyyarsa, har jami’an tsaro su ka fara bincike akansa a karshen 2014, bisa labarinsa da jaridar Birgun ta buga. Mujallar Newsweek ma ta bayyana cewa a lokacin da ‘yan sanda suka tsare shi don ya amsa wasu tambayoyi bayan da aka ga irin abubuwan da ya ke bayyanawa a shafinsa na Facebook.

Shugaban masallacin da ya ke halarta, Khalid Bellamine ya tabbatar da hakan ga VOA cewa jami’an tsaro Finland sun tuntubeshi game da Tugral. Amma sai ya shaida musu cewa bai taba hada ido da shi ba kuma ko cikin al’ummar masallacin babu wanda ya san shi.

“Abun da muka lura da shi shine, bai zuwa masallaci sai dare yayi kuma idan ya zo bai magana da kowa. Kuma da ace na yi zargin wani abu daga gareshi da tuni na shaida hakan.” inji Bellamine.

Sama: Tugral ya ziyarci gidan kwanan 7Fells a Äkäslompolo da ke kudancin Finland.


Sama: Tugral ya ziyarci gidan kwanan 7Fells a Äkäslompolo da ke kudancin Finland.

Kafin ya tafi gida hutun karshen shekara, sai ya dauki kyamararsa ta DSLR ya tafi kai ziyara babban cocin birnin Helsinki da kuma Gidan kwanan 7 Fells da ke yankin Lapland. Inda ya ce a shafinsa na facebook ya je gidan kwanan ne, “saboda mai wurin kwarrarran mai daukan hoto ne kamar ni.”

Tugral ya fito gaban Majami’ar Helsinki, wata babbar majami’ar Lutheran a ranar 17 ga watan Disambar 2014.

Ya dauke hankalinsu daga tafiyarsa

Tugral ya yada zango gida gurin ‘yan uwansa a Ankara, kafin ya kara gaba zuwa wurin jihadi a ganinsa zuwa Siriya. Ya yaudari mahaifansa da cewa zai kwana wajen abokansa na Jami’ar METU alhali ya shirya ‘yar karamar jaka da niyyar tafiya Syria.

“Na bar wa Allah komai kafin na kama hanya.” Inji Tugral, daga baya.

Ya bayyana yadda tafiyarsa ta kasance inda bayan ficewarsa daga gida sai ya tsaida wani karamin motar bas don ya rage masa hanya. Sai da ya shiga motar tukunna ya tuno cewa ya manto da kyamararsa a gida wadda ba ya rabuwa da ita. Amma kawai sai ya ga gwanda ya yi tafiyarsa din ko bada ita ba.

Ya tsallaka zuwa Syria

A wata doguwar wasikar da ya rubuta gutsun-gutsun saboda rashin ingataccen intanet da kafofin sadarwa, Tugral ya bada labarin yadda tafiyarsa ta kasance. Ya saka wannan wasikar mai taken “Gaisuwa Daga Daular Musulunci,”a Facebook ranar 25 ga watan Maris din 2015.

Ya hadu da wasu maza daga Tunisia, Libya, da kuma Saudi Arabia a garin Sanliurfa da ke bakin iyaka da Syria a kudu maso gabashin Turkiya. Mutanen ya tarad niyyarsu iri daya ne don haka, sai suka jera tare zuwa Siriya ba da izini ba. “Allah ya taimakeni da ban dauko kaya mai nauyi ba don mun sha gudu sosai na tsawon lokaci,” inji Tugral.

Wani dan Afghanistan mai dogon gashi ne ya tarbe su inda ya tuka su zuwa garin Tal Abyad. Akan hanyar suka wuce wata makekiyar tuta, da kuma suka isa sai aka saukesu a wani gida da ko wuta babu sai kyandir. Sai aka kwace fasfonsu, da duk wata na’ura da suke dauke da ita da kuma sauran kayayyakinsu. Amma kafin a amshe wayarsa, Tugral ya samu turawa ‘yan uwansa emel a gurguje.

“Rashin ingantaccen sabis ya kawo min cikas saboda dalilin intanet maras sauri, ban samu damar tura emel din dukka ba,” inji Tugral. “Ina zan je? Na fara tunani amma ko oho.”
Kungiyar IS din ta tsare su sabbin zuwan da tambayoyi daga nan sai ta ba kowa lakabin da za’a rika ambatarsa da ita. “Ba abun mamaki akayi min lakabi da Abu Huraira wato uban kyanwa da larabci.

Tugral ya rufe fuskarsa yayin da ake guguwar mai dauke da rairayi a Babban Birnin Kungiyar IS, wato Raqqa da ke Syria a ranar 6 ga watan Disambar 2015.

Tugral ya rufe fuskarsa yayin da ake guguwar mai dauke da rairayi a Babban Birnin Kungiyar IS, wato Raqqa da ke Syria a ranar 6 ga watan Disambar 2015.

Yan uwantaka da rashin walwala

Bayan ‘yan kwanaki, sai aka maida su wani gida dabam wanda ka gani ka san ganima ce don duk bangon gidan cike ya ke da ramukan harsasai. Akwai mutane kusan 20 a ciki kuma wadanda suka fito daga kasashe dabam-dabam. Daga cikinsu akwai wani tsohon kwararran dan dambe daga Jamus, wani kuma injiniya ne dan Bangladesh. Wani kuma ana sako shi daga gidan yari a Faransa ya zo nan, wani kuma sai da ya biya dalar Amurka dubu goma sha biyar daga China don yazo nan.

Bayan kwashe wasu kwanaki a nan, sai wata karamar motar bas ta kwashi Tugral da wasu sabbin dauka su takwas zuwa babban birnin daular kungiyar IS wato Raqqa. Ya bayyana irin bankwanan da suka yi da sauran mutanen da suka yi zaman tare a gidan. Yace dasu, “Sai mun hadu a Aljannah!”

Tugral ya bayyana a shafinsa na Facebook wani bidiyon da ya nuno shi yayin da ya ke nutso.

Ya zagaya birnin don gane gari yayin da yake jiran horaswan da ake bukata kafin a tura mutum filin daga. A nan ne za’a koyar da su shari’arsu da kuma fada. A wasikarsa ya bayyana cewa, “Garin na da girma kuma a cike inda za ka ga mutanen garin suna rayuwarsu lafia ba tare da an fille kan wani ba.” Garin ya burgeshi sosai saboda an haramta shan ta ba a koina a daular amma dai abun haushi yace shine hayakin konewar man dizel da ya ratsa ko’ina.

Ya kwashe makonni biyu yana cudanya da sabbin daga kasashen duniya dabam-dabam a wani gida mai sanyi sosai ba abinci sai dai kwai. Mura ta kamashi amma wannan bai dameshi ba kamar hare-haren sama da ake kawo musu akai-akai.Ya ce, “Ya ce za ka ji iska mai karfi na bugowa, a kowanne lokaci bam na iya fadowa.”

Shirin yaki

Cikin ‘yan watanni an canza masa wurin zama sau da yawa a ciki da wajen Raqqa sannan garin Homs. Ya koka da yadda gidajen suke da mutane da yawa, sanyi kuma datti. “Ya ce mutane kusan 30 su ke kwana a dakin duk haka kuma sai kawo mutane ake,” ya bayyana a wasikarsa.

Akwai lokacinma a cikin kogo su ke kwana dauke da katifu, injin wanki, da kuma janareta bada wuta.A cikin kogon har da ganima inda kamar bargunan masu tambarin Majalisar Dinkin Duniya na ‘yan gudun hijira.

An faras horas da shi a darensa na farko a kogonnan. Inda aka fara sa su tsallen kwado da wasu tsalle-tsalle cikin cabi. Yace a lokacin yana sanye ne da wata rigar sanyi da wando da ya zo da su tun daga Finland.Sai bai ji dadin yin atusayen da su ba amma babu yadda ya iya saboda haka yana bawa masu sha’awar zuwa da su zo da kaya masu duhu.

Ya zauna da wani injiniya dan Burtaniya da dansa a kogon. Ya rubuta akansu cewa, “Iliminsu na taurari da samaniya kadan ne, ni kuma ba bata lokaci na yi musu fashin baki.”

Kogon yana da wutar lantarki ba kamar birnin ba inda wurare kadan ne ke da wuta. Ya shaida cewa a dalilin haka ne ka kan iya kallon samaniya sosai a daular Kungiyar IS.

Fargabar hare-haren sama

Ana ta kai musu hare-haren sama, da jiragen yakin gwamnatin Bashar Al Assad. ”Kullum sai sun kawo mana hari. Wani bam mai iska ya na zuwa kusa da mu sosai, kararsa sai ya kashewa mutum kunne kuma a inda ya fadi ya bar rami mai zurfi kusa da mu.

A nan har zaman kogon ya gundireshi inda yake kokawa da matsalolin daular kamar rashin tsaftace muhalli, rashin tsari mai kyau kuma wasu sabbin zuwa a na shakkan niyyarsu. Wani dan Moldova kuma tsohon mamban wata kungiya da ke da dangantaka da al-Qaida wato Al-Nusra ya bayyanawa Tugral cewa, “Wasu daga cikin mayakan zuwa suke da niyyar samun duniya ba don lahira ba saboda suna samun kudi da gurin zama daga daular IS.”

Amma wannan bai canza mai fatansa na makoma mai kyau inda ya rubuta cewa, “E, na sani cewa akwai kalubalai tattare da daular amma laifin mutane ne ba nata ba. Abubuwa basu tafiya yadda ya kamata, tsafta ba ta damesu kuma ba a damu da bin ka’idojin bin hanyar mota ba. Amma sannu a hankali muna kokarin canza duk wadannan musamman ma ta gefen baki” – wato lakabin da ake yiwa mayaka daga wasu kasashe.

Sama: Tugral tsaye daga hagu tare da wani mayakin IS a Raqqa, a ranar 9 ga watan Yulin 2015.Garin Deir ez-Zor ya zamo kango duk kowa ya gudu bayan da fada tsakanin dakarun gwamnati da mayakan IS ya yi tsanani, inji Tugral a shafinsa na Facebook bayan wani hoto da ya sa a ranar 9 ga watan Agustan 2015.

Sama: Tugral tsaye daga hagu tare da wani mayakin IS a Raqqa, a ranar 9 ga watan Yulin 2015.


Garin Deir ez-Zor ya zamo kango duk kowa ya gudu bayan da fada tsakanin dakarun gwamnati da mayakan IS ya yi tsanani, inji Tugral a shafinsa na Facebook bayan wani hoto da ya sa a ranar 9 ga watan Agustan 2015.

Filin daga

Bayan da suka yi kusan wata daya zaune a kogon sai aka maida shi da wasu sabbin zuwa 5 kwamandoji su ma suka shiga sahun mayakan kungiyar.

A nan ne komai ya canza inda aka basu wani masauki a wajen garen Homs. Kowa aka ba sabon bargo, su ka koma ana yanka musu rago kowanne mako ana kuma dafa musu abinci irin na gida da suka baro. “A kullum sai mun ci ayaba da lemu har da fakitin cakulet guda 4.”

An fara turashi yaki don bada agajin gaggawa ga mayakansu da suka jikkata saboda horaswan da ya samu na hakan a Jami’ar METU. “Na zamo likita don ilimin kiwon lafiya ko yaya mutum ya sani, yana da amfani a nan,”inji Tugral.

“A nan ne karon farkon da na fara jin karar harbe-harbe bindigogi kusa da inda nake,” Inji shi. A lokacin wai sai suka boye bayan wasu tsaunuka suna jin karar tanka da manyan bindigogi, ruwa da iska mai sanyi duk a kan kafin aka basu izinin janyewa. Tantinsu da suka mayar wajen kula da mutanensu da suka jikkata kuma a lokacin mutane biyu sun mutu, shida kuma sun jikkata.

Ya kare ayyukansu na rashin tausayi

Sun kwana suna fafatawa daga karshe kuma sun yi nasara inji Tugral inda suka samo ganimar tankoki biyu, motar daukar kaya da wasu gurnati masu roka da kuma kawunan mutane uku.

Ya kare yadda kungiyar ta ke fille kan mutane a shafinsa na Facebook bayan da abokinsa na Jami’a, Boratac ya soke shi da cewa, “Me yasa yake goyon bayan kungiyar da take yankan rago wa mutanen da basu san hawa da sauka ba? Wannan ai zaluncine karara!”

Sai ya bashi amsar cewa ai wannan shine hukuncin da ake yiwa magoya bayan gwamnatin Siriya wadanda suka kashe mutane da basu da laifi, ko wadanda basu bin su ko kuma wadanda suka zamo bayin Amurkawa. Ya kuma kare yadda kungiyar take daukan mata a matsayin kwarakwarai musamman ma tsirarun kiristoci ‘yan kabilar Yazidi.

Ya kuma ce fille kawunan mutane wata dubara ce mai amfani, “Wannan kawai amfaninsa don ya tsoratar da makiya yadda zasu su gani su ji tsoro.”

An bashi mata

Ya raunata a wata arrangama da mayakan kurdawa a garin Tal Abyad a farkon watan Afrilun shekarar 2015 inda ya tafi Raqqa don jinya.

Tugral sa’adda yana  jinya a arewacin garin Tal Abyad  bayanda ya ji rauni . An sa hoton a intanet a ranar 17 ga watan Afrilun 2015.

Tugral sa’adda yana jinya a arewacin garin Tal Abyad bayanda ya ji rauni . An sa hoton a intanet a ranar 17 ga watan Afrilun 2015.

Bayan wata guda sai ya auri wata ‘yar Turkiyya mabiya kungiyar, Aisha Zevra Et-Turki.

A facebook, ya bayyana yadda ake biyan su, inda mayaki gwauro ya ke karban dalolin Amurka 100 kowacce wata. Ana yiwa mayakan da suka zo daga kasashen waje sharadin kada a wuce watanni hudu da zuwa kafin yin aure. Kungiyar tana baiwa ma’aurata gida da kudin don rike iyali.

Bayan aure sai ya rage yake amfani da kafofin sadarwa sosai har abokinsa Boratac ya nemeshi da nufin ko zai iya lallashinsa ya dawo gida Turkiya. “Yace ba komai, kawai amaryarsa ne ke kishin yadda ya ke bata lokaci kan kafofin sadarwan.Ban san ko ba’a ya ke ko da gaske ya ke,” inji Boratac.

Daga bayan ya koma amfani da shafukansa na Facebook da Twitter jifa-jifa inda ya bayyana yadda yayi zurfi cikin akidar kungiyar. Ya kuma koka da yadda hare-haren sama da hadin gwiwar Syria da Rasha ko kuma Amurka ke ta kashe fararen hula. Ya kan yi kokarin jan hankalin mutane don su yi komai bisa yadda shari’a ta shimfida daga yadda ya kamata a ci abinci zuwa yadda ake shiga bandaki.

Ya kuma soki larabawa Siriya da cewa ko karatun Qur’ani basu iya ba kuma basu iya gaisuwa kamar yadda addini ta tanada. “Ya na ci min rai idan nayi musu sallama sai dai kawai su amsa da yawwa sannu.” Ya rubuta a shafinsa na intanet.

Kafirai sai wutar jahannama ba gargada

Duk da yadda ya sauya sosai, bai daina son kimiyya ba. Akai-akai ya saka tsaffin hotunan taurari da samaniya da ya dauka a da. Ya kan yi tsokaci akan ilimin duwatsu, kampanonin sarrafa magani ko kuma yadda matattarar bayanan komfuta ka iya zamowa ba iyaka nan gaba kamar taurari.

Akan shafinsa na Twitter kuma, ya yabi masana kimiyya kamar su marigayi Richard Feynman amma yana musu wa’azi da cewa, “Ku karbi musulunci kafin mutuwa ta zo muku.” Ya taba haduwa kuma suka dauki hoto da wani Ba’amurke mai lambar yabo ta Nobel kan Physics, Walter Kohn. Amma da mutumin ya rasu, sai ya sa a shafinsa na Twitter cewa, “Ya halaka tunda ya mutu ba musulmi ba.”

Tugral ya dauki hoto da wani kwararre mai nazarin ilimin kiddiga, Walter Kohn a wani hoton da ba a san sa’adda aka dauka ba kuma a inda aka dauke shi.


Tugral ya dauki hoto da wani kwararre mai nazarin ilimin kiddiga, Walter Kohn a wani hoton da ba a san sa’adda aka dauka ba kuma a inda aka dauke shi.

Mutuwa ta iske Tugral da farkon watan Agusta bayan wata arrangama da kurdawa wadanda Amurka ta marawa baya a arewacin Raqqa. Kungiyar IS ta shaida hakan ne a shafinta na kafofin sadarwa kuma ya rasa ransa ne yayin da kungiyar ta ke rasa wuraren da ke hannunta.

A wata takaitaccen hirar Muryar Amurka da mahaifinsa sa’adda wakilinmu ya je gidansu a Ankara, ya fadi cewa matar Tugral ce ta tabbatar musu da rasuwarsa ta waya kuma ta ce an birneshi a Syria. Shi kuma ya na ta kokarin samu a dawo da gawarsa gida inda ya bukaci jami’ai da suyi bincike a kai.

“Bamu san yadda ya mutu ba saboda haka mun kai karar ofishin mai shigar da kara kuma muna jiran amsarsu.”
Bai kara cewa komai ba bayan hakan kuma sauran ‘yan uwansa basu amince ayi hira da su ba.

Wani hoto da aka sa a shafin kafofin sada zumunta na kungiyar IS, ya nuna gawar Tugral bayan rasuwarsa a Raqqa, Siriya.

Wani hoto da aka sa a shafin kafofin sada zumunta na kungiyar IS, ya nuna gawar Tugral bayan rasuwarsa a Raqqa, Siriya.

Allah ya hadamu a lahira

Ya shigar da sakonsa na karshe a Facebook ranar 31 ga watan Agusta, kusan wata daya bayan rasuwarsa inda ya ke cewa:

“Idan ba ku sake jin daga gareni ba to ku sani cewa rai yayi halinsa kuma na bar duniyar. Ku yi min addu’a Allah ya amsheni a matsayin shahid. Wannan sako ne mai tura kansa wato otomatik. Allah ya hadamu a lahira.”

Har yanzu shafinsa na nan amma na Twitter an rufeshi kwanannan. Inda Kampanin Twitter ta shaidawa Muryar Amurka cewa ta rufe shafukan masu yada ayyukan ta’addanci na sama da 360,000, musamman wadanda ke da dangantaka da Kungiyar IS tun tsakiyar shekarar 2015.

Wani dan Turkiyya mai bincike kan harkokin siyasa da tsaro a Jami’ar Keele da ke Burtaniya, Salih Dogan yayi kiyasta dubban ‘yan Turkiya ne suka shiga kungiyar IS. Ya ce, “Kowa da dalilinsa amma yawancinsu a dalilin aika-aikan da ke faruwa a yankin Damaskus da ke Siriya ne ya kaisu ga shiga kungiyar.” Wasu kuma kila don sun tashine a gidan masu ra’ayin riqau, ko an musguna musu, ko kuma kawai tsabar tawayene ko don neman abun duniya.

“Da ciwo ka ga matasa sun bata rayuwarsu hakan.” Inji Dogan, ya kuma kara da cewa, “Abun lura anan shine, dole mutum sai ya cika gibin da ke zuciyarsa da hankalinsa ta yadda ba zai fadawa irin wannan makomarba.”

A garin Raqqa da ke hannun Kungiyar IS a Siriya, Tugral ya koyar da yara dabarun hangen sararin samaniya. Ya saka hoton ne a Twitter ranar 5 ga watan Mayun 2016.

A garin Raqqa da ke hannun Kungiyar IS a Siriya, Tugral ya koyar da yara dabarun hangen sararin samaniya. Ya saka hoton ne a Twitter ranar 5 ga watan Mayun 2016.

Har yanzu abokin Tugral na jami’a, Boratac yana tunanin yadda aka yi haka ta faru.

Akwai wani lokacin da na taba ganin wani haske da ba mu gane kansa ba, har Boratac ya yi tunanin ko bakin halittune daga wata duniyar. Tugral ya saurareshi sannan ya je yayi bincike har ya gano menene. “Sai ya zo ya ce min, kai sakarai ai tauraron dan Adam ne! Ya ilmantar da ni kan illar yanke hukunci da sauri kafin tantancewa,”inji Boratac. Shi yasa ya ke mamakin yadda akayi farfagandan kungiyar IS ya rudi abokinsa.

“Ina mamakin yadda akayi har ya kauce hanya. A da mutum ne mai ban da dariya bai dauki duniya da zafi ba. Daga baya kuma ya zamo mutum mai goyon bayan fillewa mutane kawuna,” Inji Boratac.

Abokinsa na jami’ar METU, Celik ya na ganin a dalilin kasa daidaita mabanbantan ra’ayoyin ne ya jawo hakan. “Tunaninsa birkicewa yayi – ga addini a hannu guda, kimiyya kuma a dayan. Duniyar ta zamo cike da duhu kuma na fahimci hakan tun kafin ya shiga kungiyar IS.

Uzay Bulut, Kasim Cindemir da kuma Rikar Hussein daga Sashen sa ido kan tsaurin ra’ayi na Muryar Amurka a Washington DC tare da Yildiz Yazicioglu a Ankara Turkiyya ne suka hada hannu aka rubuta wannan labari. Carol Guensburg ce ta rubuta kuma Maryam Bugaje tare da Ibrahim Ahmed ne suka fassarashi zuwa Hausa. Duka hotunan an samo ne daga shafukan Rasid Tugral na Facebook da Twitter sai dai inda shaida dabam.

Tugral yana kallon Milky Way galaxy yayin da ya ke kusa da Cibiyar Nazarin Samaniya ta Kasa ta TUBITAK.